Gwamnatin Najeriya ta ce ba za a iya kwaso daliban Najeriya da ke karatu a kasar Sudan a halin yanzu.
Gwamnatin ta bayyana haka ne a yayin da daliban Najeriya da ke karatu a Sudan suka roke ta da dawo da su gida, bayan kazamin fada ya barke a kasar.
- Dalibai sun daina zuwa makaranta sun koma Harkar Yahoo
- Rikicin Sudan: Fada ya barke bayan sanarwar tsagaita wuta
Kimanin mako biyu ke nan ana gwabza fada a kasar tsakanin wasu bangarori biyu ke rikici da juna kan shugabancin kasar.
Rikicin bangarorin biyu da ke goyon bayan wasu janar-janar na soja kan shugabancin kasar, ya yi ajali da kuma jikkata daruruwan mutane.
Lamarin dai ya kai ga kasashen duniya sun yi kira ga bangaorin da su kai zuciya nesa.
Aminiya ta ruwaito cewa an ci gaba da luguden wuta har da jiragen yaki a Khartoum, fadar kasar jim kadan bayan sojoji da ’yan tawayen kasar sun amince da tsagaita wuta na kwana uku.
An yi luguden wutan ne a ranar Juma’a da ake bikin Karamar Sallah, ranar da bangarorin suka amince su tsagaita wuta na kwana uku domin ba wa ’yan kasar damar yin bukukuwan Karamar Sallah.
Rundunar sojin Sudan ce ta sanar da amincewarsu da tsagaita wuta a tsakaninsu da ’yan tawaye daga ranar Juma’a, wadda ta kasance ranar Karamar Sallah a kasar.
Sanarwar da sojojin suka fitar ta ce, “Sojoji za su mutunta duk sharuddan yarjejeniyar tsagaita wutan da kuma dakatar da duk wani matakin soji da ke iya kawo tasgaro”
Sun sanar da haka ne bayan a safiar ranar ’yan tawayen RSF da suka shafe mako guda suna gwabza yaki da sojojin sun amince su tsagaita wuta na tsawon kwana uku.