✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin siyasa ya yi awon gaba da kujerar Firaministan Italiya

Ya mika takardar ajiye aiki ne ranar Alhamis

Firaministan Kasar Italiya, Mario Draghi, ya sauka daga mukaminsa a sakamakon rikita-rikitar siyasar kasar da ta ki ci, ta ki cinyewa.

Mario shugaban gwamnatin Italy wanda yake rike da mukamin Firaminista ya mika takardar sauka daga mulki ne ga Shugaban Kasar, Sergio a Milan babban birnin kasar.

Tsohon Firaministan ya sauka ne bayan yarjejeniyar kawancen dake tsakaninsu da wasu manyan jam’iyyun kasar ya wargaje ga kuma matsalar tattalin arziki da tsadar rayuwa.

A wata sanarwa da Fadar Shugaban Kasar ta fitar ranar Alhamis, ta ce Shugaban Kasar ya karbi takardar sauka daga mulki, amma Draghi ya ci gaba a matsayi na rikon kwarya.

Mista Draghi dai tsohon shugaban Babban Bakin Turai ne, wanda aka zabe shi ya zama Firaministan kasar a shekarar 2021.

A zamanin mulkinsa, Draghi ya yi fama da matsalar tattalin arzikin kasar, da kuma annobar Korona da ta dakile walwala da harkokin kasuwanci.

Rikicin siyasa tsakaninsa da hadakar jam’iyyun da suka yi kawance, da ya ki ci, ya ki cinyewa ta sa ya yar da kwallon magwaro don ya huta dac kuda.

Hakan ta sa yanzu a dole a gudanar da sabon zabe a kasar.