✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe shugaban Lakurawa, Maigemu a Kebbi

Rahotanni sun bayyana cewar an kashe shugaban Lakurawan ne a musayar wuta da jami'an tsaro.

Jami’an tsaro da ’yan sa-kai sun kashe shugaban ’yan ta’addan Lakurawa, Maigemu, a Jihar Kebbi.

Daraktan Tsaro na Jihar Kebbi, AbdulRahman Usman Zagga ne, ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a cewa an kashe Maigemu a ranar Alhamis.

Ya ce an kashe shi ne yayin musayar wuta da jami’an tsaro a garin Kuncin Baba da ke Ƙaramar Hukumar Arewa.

Mutuwarsa ta zo ne mako guda bayan da Gwamna Nasir Idris ya kai ziyarar jaje ƙauyukan Bagiza da Rausa Kade, inda ’yan ta’adda suka kashe mutum shida.

“Ƙoƙarin gwamna ya haifar da ɗa mai ido, domin yanzu an kashe wannan babban shugaban ’yan ta’adda. Gawarsa tana nan a matsayin shaida,” in ji Zagga.

Ya yaba wa gwamnan bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da tsaro da kuma tallafin da yake bai wa jami’an tsaro a kai a kai.

Zagga ya kuma roƙi jama’a da su ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro ta hanyar ba su bayanai da kuma kai rahoton duk wani abun zargi domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.