Rahotanni daga Jihar Bauchi sun ce mutum guda ya mutu, wasu 14 sun jikkata a rikicin siyasa da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyun PDP da APC a garin Duguri, mahaifar Gwamna Bala Mohammed.
An yi arangamar ne yayin da APC ke gudanar da yakin neman zaben gwamna, sa’o’i 24 bayan ’yan takarar kujerar a jihar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnoni da na ’yan majalisar jiha da ke tafe.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, ya kara da cewa, an lalata motoci kirar sharon guda biyu da kuma A Daidaita Sahu bakwai.
Ya ce, “Dawowarmu ke nan daga Duguri inda muka kai ziyarar gani da ido wurin da rikicin ya faru karkashin jagorancin Kwamishinan ’yan sandan jihar, Alhassan Aminu.”
A cewarsa, kwamishinan ’yan sandan jihar ya umarci Mataimakin Kwashina mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuka ya gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin.
A nasa jawabin, Darakatan Yada Labarai na APC a jihar, Salisu A. Barau, ya yi zargin magoya bayan PDP ne suka bude wa tawagar yakin neman zabensu na gwamna wuta.
“Wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka bude wa tawagar dan takarar gwamnan na APC, Air Marshal Sadique Baba Abubukar (mai murabus) wuta a Duguri, mahaifar Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed,” in ji shi.
Yayin da bangaren PDP, ta bakin Darakta-Janar na yakin neman zaben Gwamna Bala Mohammed, Farouk Mustapha, ya zargin ’yan daban APC a ne suka kai musu hari.