Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta rufe harabar majalisar dokokin jihar, bayan zabar shugabanni biyu.
Kakakin rundunar, Ramhan Nansel ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Maiyaki Mohammed-Baba ne ya bayar da umarnin rufe majalisar domin kauce wa tashin rikici.
- Majalisa Ta 10: Sanatoci 75 na goyon bayan Akpabio —Ndume
- NAJERIYA A YAU – Shin Buhari Zai Iya Rayuwa A Daura?
A ranar Talata ne, zababbun ’yan majalisar jihar suka kasu gida biyu, inda kowane tsagi ya zabi shugabansa.
Yayin da wani bangare mai mutun 11 ya zabi Ibrahim Abdullahi, a matsayin shugabansa, daya bangaren mai mabobi 13 ya zabi Daniel Ogazi a zauren majalisar dokokin jihar.
Aminiya ta ruwaito cewar magatakardar majalisar, Ibrahim Musa, ya dage taron kaddamar da majalisar karo na bakwai wanda aka shirya gudanar da shi a ranar Talata.
Da yake mayar da martani game da lamarin, Abdullahi ya ce sake zabensa ya biyo bayan tsarin da ya dace da kuma tanadin kundin tsarin mulki.
Abdullahi ya yi martanin ne bayan irin barnar da aka yi a harabar majalisar kan rikicin shugabancin.
Ya ce duk wani bikin rantsuwa da aka yi idan ba magatakardar majalisar ne ya yi ba, to ba shi da inganci.
Kakakin majalisar ya bukaci mutane da su yi watsi da duk wata dakatarwar da tsagin Daniel Ogazi ya jagoranta.
“Ta yaya za ku dakatar da mambobin da ba sa cikin bikin rantsar da ku?” Abdullahi ya tambaya.