Sufeta Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya rufe ofishin jam’iyyar APC na kasa biyo bayan rikicin shugabancin jam’iyyar.
Mohammed Adamu ya aike wa jam’iyyar umuarnin rufe ofishin nata ne a ranar Talata, ta hannun Kwashinan ’Yan Sandan Birnin Tarayya Bala Ciroma, tare da umartar ma’aikata su fice daga harabar ofishin nan take.
’Yan cikin gida a jam’iyyar sun ce Babban Sufeton ya kira taron ganawa da Kwamitin Gudanarwa na Kasa na jam’iyyar game da rikicin shugabancinta.
Suna hasashen tattaunawar za ta mayar da hankali ne a kan nadin da Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar na Kasa kuma Mataimakin Shugaba (Kudu-maso-kudu), Prince Hilliard Eta ya yi wa Worgu Boms a matsayin sabon Mataimakin Sakataren Jam’iyyar domin maye gurbin Victor Giadom, wanda Jam’iyyar ta dakatar.
Jami’iyyar APC ta fada cikin rikicin shugabanci a ‘yan kwanakin nan bayan Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da dakatar da Adams Oshiomhole daga zama Shugabanta na Kasa.
Lamarin ya haifar da wata baraka a shugabancin jam’iyyar inda Giadom ya ayyana kansa a matsayin Shugaban Riko, sabanin sanarwar Kwamitocin Gudanarwa da na Zartarwa na Kasa cewa Abiola Ajimobi ne shugaba na riko.
Ajimobi shi ne Mataimakin Shugaba (Kudu-maso-yamma), amma yana kwance a asibiti ba shi da lafiya.
Sakamakon haka Kwamitin Gudanarwa ya sa Prince Hilliard Eta ya yi aiki a matsayin mukaddashinsa.
Bayan dakatar da Oshiomhole, Giadom ya samu umurnin kotu cewa ya rike kujerar na dan lokaci, kafin daga bisani wata kotu ta soke hukuncin tare da umartar sa da ya daina gabatar da kansa a matsayin shugaban jam’iyya.
Hakan ta yi sanadiyar dakatar da Giadom saboda abin da jam’iyyar ta kira zubar da kimarta, matakin da ya kira ‘abin da dariya’, yana mai cewa dole a kira taron Kwamitin Zartarwa na Kasa domin yi wa tufkar hanci.