✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin Shugabanci: Kotu ta tabbatar da Achida a matsayin Shugaban APC a Sakkwato

Kotun ta sake tabbatar da shi a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar a Jihar

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Sakkwato ta tabbatar da Isa Sadiq Achida a matsayin Shugaban jam’iyyar APC na Jihar.

Da ya ke yanke hukunci a ranar Laraba, alkalin kotun, Mai Shari’a James Omotosho, ya yi watsi da karar da bangaren APC karkashin Mainasara ya shigar.

A cewarsa, ya kamata a shigar da karar a cikin kwanaki 14 da yanke hukuncin kotun daukaka kara da ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun Abuja ta yanke kan lamarin.

Mai shari’ar ya kuma yi watsi da cewa ba a gudanar da taron da ya samar da kwamitin zartarwa karkashin jagorancin Mainasara a sakatariyar jam’iyyar da ta yi watsi da ka’idojin da APC ta gindaya na gudanar da tarukan majalisar jihar.

Kazalika, ya ce bisa rahoton hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Achida ne kadai aka amince da shi a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar.

A baya mai shari’a Omotosho ya yi watsi da matakin farko da lauyan ya shigar a kan Achida.

Bayan taron da aka gudanar a jihar a shekarar da ta gabata, shugabanni biyu ne suka fito takarar shugabancin APC a jihar, Isa Sadiq Achida, wanda Sanata Aliyu Wamakko ya mara wa baya da kuma Mainasara Abubakar Sani, wanda Sanata Abubakar Gada ya mara wa baya.

A baya dai wata babbar kotun Abuja ta ayyana bangaren Mainasa a matsayin zababben shugaban jam’iyyar APC a Sakkwato, amma kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da kotun ta yanke.

Bayan hukuncin kotun daukaka kara ne bangaren Mainasara ya garzaya babbar kotun tarayya da ke Sakkwato, inda suka shigar da sabuwar kara.