✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin sarauta ya ci rayuka 2 da kadarori a Osun

Gwamnatin Osun sun tabbatar da mutuwar mutum biyu a rikicin sarauta tsakanin al'ummomin Orile-Owu da Araromi-Owu a Karamar Hukumar Ayedade

Mahukunta Osun sun tabbatar da mutuwar mutane biyu a rikicin sarauta tsakanin al’ummomin Orile-Owu da Araromi-Owu da ke Karamar Hukumar Ayedade a Jihar Osun.

Wata majiya mai tushe ta shaidawa Aminiya cewa rikicin ya kazance ne a ranar Talata a lokacin da wasu matasa suka kona Fadar Olowu na Araromi.

Lamarin ya haifar da kaurewar fada a tsakanin bangarorin biyu da ya yi sanadin kone-konen gidaje da motoci da toshe hanyoyin zirga-zirgar abubuwan hawa a garuruwan biyu masu makwabtaka da juna.

Majiyar ta ce zaben daya daga cikin al’ummomin biyu a matsayin Baale wato hakimin garuruwan ne ya haifar da wannan rikici.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, mai ba gwamna shawara a kan tsaro, Barista Samuel Ojo, ya ce “yau kwanaki uku ke nan da aka fara rikicin da ba mu zaci zai kazance kamar haka ba.”

Ya ce mutane biyu sun rasa rayuka kuma an yi kona gidaje da kadarori a lokacin rikicin da Gwamna Ademola Adeleke ya bayar da umarnin girke jami’an tsaro domin kare lafiyar al’ummomin biyu.

Sanarwar da kwamishinan yada labarai, Oluomo Kolapo Alimi ya sanya wa hannu, ya ce Gwamna Adeleke ya bayar da umarnin dakatar da dukkan shirye-shiryen nada sabon Hakimi a wannan yanki.

Ya ce Gwamnan ya nemi bangarorin biyu su kwantar da hankali tare da girmama doka da oda domin samar da zama lafiya.

Kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Osun, Yemisi Opalola, ta tabbatar da aukuwar lamarin, da ta ce tuni aka girke jami’an tsaro a sassa daban-daban na garuruwan Orile-Owu da Araromi-Owu domin tabbatar da tsaron lafiyar al’umma.