Kasar Amurka na shirin kai wa Ukraine dauki da makamai don kare kanta daga barazanar kai hari daga kasar Rasha.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, ya ce kasarsa ta yi alkawarin tallafa wa Ukraine da makaman da take kerawa na cikin gida don kare kanta daga duk wata barazana musamman daga Rasha.
- Mahaifiyar Dahiru Mangal ta rasu
- Najeriya A Yau: Yadda Tsaro Da Tattalin Arziki Za Su Shafi Zaben 2023
Wannan dai na zuwa ne bayan kasashen Arewa maso Gabashin Turai uku sun mika wa Amurka bukatar hadin gwiwa ta neman tallafa wa Ukraine da manyan makamai.
A halin da ake ciki yanzu dai dubban dakarun Rasha na jibge a kan iyakarta da Ukraine dauke da muggan makamai suna jiran umarnin afka wa kasar.
Ko a shekarar da ta wuce, sai da Gwamnatin Joe Biden, ta tallafa wa Ukarine da kudi har Dala miliyan 450 don karfafa fannin tsaronta, sannan ta kara mata wata Dala miliyan 200 a farkon makon nan.