✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin PDP: Wike da wasu Gwamnoni 5 sun ziyarci Gwamnan Bauchi

Ganawar na da alaka da rikicin cikin gida na PDP

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike tare wasu takwarorinsa su biyar na jam’iyyar PDP sun isa Jihar Bauchi ranar Laraba.

Gwamnonin sun tafi Bauchin ne domin ganawa da takwaransu na Bauchi, Bala Mohammed.

Gwamna Bala da kansa ya tarbi manyan bakin nasa a Babban Filin Jirgin Sama na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, daga nan suka dunguma zuwa Fadar Gwamnatin Jihar inda a nan za su tattaunawa.

Wannan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan Gwamna Mohammed ya yi tattaunawar neman sulhunta tsakani tare da dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a Abuja.

Kafin wannan lokaci, Mohammed ya aika da wasika zuwa ga Shugaban PDP na Kasa, Iyorchia Ayu, inda ya yi barazanar ficewa daga Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar saboda mugun halin da ya ce ana nuna masa.

Da alama barazanar da Gwamnan Bauchin ya yi ta kara tsananta rashin jituwar da ke tsakaninsu da Gwamna Wike da Atiku Abubakar da kuma Shugaban PDP na Kasa.

Bayanai sun nuna Wike da sauransu sun ziyaraci Mohammed ne don zawarcin ya dawo cikinsu su hada kai don cimma manufofinsu.

%d bloggers like this: