Wata kotun majistare tsare wasu mutum shida kan kashe wani matashi da salwantar shanu 188 a wata arangama tsakanin makiyaya da manoma a Karamar Hukumar Bagwai a Jihar Kano.
Kotun, karkashin jagorancin Talatu Makama, ta tsare su ne kan zargin kisan wani Shehu Abubakar mai shekara 25, a rikicin makiyaya da manoma a yankin Sarkin ’Ya.
- DAGA LARABA: Mahimmancin Barin Wasiyya Tun Kana Da Rai
- ’Yan bindiga sun sace sarki daga fadarsa a Taraba
An kai matashin asibitin Bagwai bayan faruwar lamarin inda a can aka tabbatar da mutuwarsa.
Masu gabatar da kara sun shaida wa kotu cewa wadanda ake tuhumar sun tare wata hanya don hana makiyayan da ciyar da dabbobinsu.
An zarge su da kashe shanu 97 tare da sanadin bacewar wasu 91 da kuma koma babura kirar Boxer guda tara.
Mai gabatar da karar ya bayyana cewa an kiyasta darajar shanun da aka kashe da kuma wadanda suka bace a kan miliyan 102.7.
Ya kara da cewa ayyukan wadanda ake tuhuma sun saba wa sashe na 97, 221 da 329 na dokar hukunta manyan laifuka ta Jihar Kano.
Sai dai bayan karanta tuhumar, wadanda ake zargin sun musanta aikatawa.