Manajan-Daraktar Rediyon Jihar Kano, Hajiya Sa’adatu Babaji, ta dakatar da Shugaban dakin Karatu na gidan rediyon, Alhaji Habibu Musa Gwangwazo daga aiki, bisa zarginsa da laifin sanya wani faifan wakar da aka yaba wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso.
Aminiya ta kalato cewa, haka ita ma wata mai gabatar da shirye-shirye a gidan rediyon, Hajiya Furera Umar, wacce take bakin aiki a lokacin da aka sanya wakar, an ba ta takardar tuhuma.
Wani ma’aikaci a gidan rediyon, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce: “Muna cikin tsaka-mai-wuya a gidan rediyon nan. Shi ma’aikacin da aka dakatar daga aiki, shi ne Shugaban Laburarenmu, kuma wai laifinsa shi ne, saboda ya zabo wani faifan waka, wacce a cikinta ake yabon tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso.”
Duk kokarin da Aminiya ta yi domin samun bayani daga Manajan-Daraktar gidan rediyon, Hajiya Sa’adatu Babaji ya ci tura, domin kuwa ta ki daukar kiran wayar da ta yi mata da dama kuma ta ki maido da amsar tambayoyin da aka yi mata a rubuce, ta hanyar sakon wayar.
Rikicin Kwankwaso da Ganduje: An dakatar da dan jarida daga aiki
Manajan-Daraktar Rediyon Jihar Kano, Hajiya Sa’adatu Babaji, ta dakatar da Shugaban dakin Karatu na gidan rediyon, Alhaji Habibu Musa Gwangwazo daga aiki, bisa zarginsa da…