Akalla mutane 10 suka rasa rayukansu sakamakon wani artabu tsakanin mambobin kungiyoyin asiri a Jihar Osun da ke Kudancin kasar.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya zanta da wasu mazauna yankin da suka shaidi lamarin, inda suka ce, an kwashe kwanaki biyu ana artabun tsakanin kungiyoyin asirin da suka yi ta harbe-harben bindiga.
- An dakatar da Mourinho saboda daga wa alkalin wasa murya
- Aisha Buhari ta kai ziyara Majalisar Tarayya
Rahotanni sun ce, wata kungiya ce ta fara kai wa abokiyar gabarta farmaki a yankin Irojo a cikin daren ranar Talata, kafin daga bisani ita ma ta mayar da martani.
Wannan tashin hankalin ya tilasta wa mazauna yankin rufe shagunansu, yayin da al’umma suka yi lamo cikin gidajensu domin tsira da rayukansu, inda tituna da unguwanni suka kasance wayam babu kowa.
Bayanai na cewa, ana yawan samun irin wannan rikicin tsakanin kungiyoyin daba a jihar ta Osun mai dadadden tarihi a kasar Yarbawa, lamarin da ya sa jama’a ke rayuwa cikin fargaba a mafi tarin lokuta.