✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Kaduna: ‘Yan sanda sun gabatar da mutum 97 a kotu

Hukumar ‘Yan Sanda a Jihar Kaduna sun kama tare da gabatar da mutum 97 da ake zargi da hannu a tashin hankalin da ya faru…

Hukumar ‘Yan Sanda a Jihar Kaduna sun kama tare da gabatar da mutum 97 da ake zargi da hannu a tashin hankalin da ya faru a jihar wanda ya faro daga yankin Kasuwar Magani da ke Karamar Hukumar Kajuru.

A cikin takardar manema labarai da hukumar ta fitar a makon da ya gabata, wanda kuma ya ke dauke da sa hannun Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Ahmad Abdurrahman, ya bayyana cewa da farko hukumar ta fara kama mutum 22 ne da ke da alaka da rikicin Kasuwar Magani kafin daga baya ta sake damke mutane 23 da adadinsu ya kai 45 inda ta gabatar da su a Kotun Majistiri ta 1 da ke titin Ibrahim Taiwo a Kaduna.

Daga baya kuma kamar yadda hukumar ta bayyana, ta sake kama mutane 52 da adadinsu ya kai 97 wadanda ta ce su ma za ta mika su ga kotu don ci gaba da bincike da kuma fara shari’a.

Kwamishina Ahmad Abdurrahman, ya bayyana a cikin sanarwar, irin kokarin da hukumarsu ke yi wajen ganin ta zakulo dukkanin masu hannu cikin tashin hankalin da ta yi sanadiyyar rasa rayukan jama’a a cikin jihar.

A ci gaba da kokarin da jami’an ‘yan sanda ke yi don tsarkake jihar daga hannun batagari, kwamishinan ya ce sun kama mutum 27 da ake tuhumarsu kan laifuffuka daban-daban da suka hada da fashi da makami da fyade da mallakar makami da garkuwa da mutane da sauran laiffufuka.

A karshe kwamishinan ya roki jama’a da su rika sa ido tare da taimaka wa jami’an tsaro da dukkan bayanan da za su taimaka masu wajen magance marasa da’a da sauran ayyukan batagari a fadin jihar baki daya.