✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin kabilanci ya ci mutum daya a Abuja

Ba gaskiya ba ne jita-jitar da ake yadawa cewa Fulani makiyaya ne suka kai hari Abuja.

’Yan sandan Abuja sun tabbatar da mutuwar mutum daya a wani rikici da ya barke a unguwar Gwarimpa.

Mai magana da yawun ’yan sandan Abuja SP Josephine Ade ta bayyana cewa rikicin ya barke tsakanin wasu babilu guda biyu mazauna wani yanki da ake kira Gwarimpa Village.

Bayanai sun ce tun ranar Asabar ne tarzomar ta fara bayan kabilar Gbagyi sun yi yunkurin korar wasu da suke zargin suna dillancin kwayoyi a yankin.

’Yan sanda sun ce mutumin da aka kashe matashi dan shekara 20, kuma ya rasu ne sanadin raunukan da aka ji masa a jiya Lahadi.

Sun ce rikicin ya sake tashi da safiyar Litinin, bayan Hausawa sun samu labarin rasuwar dan uwan nasu da aka kai asibiti sanadin raunukan da ya ji, ko da yake sun yi kokari, a cewar Josephine sun shawo kan al’amuran.

Ta ce ba gaskiya ba ne jita-jitar da ake yadawa cewa Fulani makiyaya ne suka kai hari unguwar Gwarimpa a cikin birnin Abuja.

Wasu kafofin yada labarai sun ba da rahoton cewa fadan kabilanci ya yi sanadin mutuwar mutum uku, zargin da mai magana da yawun ’yan sanda ta ce shi ma babu kamshin gaskiya a ciki.

BBC