’Yan kasuwar man girki ta Galadima Road a Jihar Kano na jimamin asarar da suka tafka saboda banka wa motocinsu wuta da ’yan haramtacciyar Kungiyar ’Yan Awaren Biyafar ta IPOB suka yi.
’Yan IPOB dai sun banka wa motocin nasu ne da ke dauke da manja wuta a yankin Kudu maso Gabas, a daidai lokacin da ake ci gaba da tarzoma a can.
- Buhari na neman majalisa ta amince da sabon shugaban Sojin Kasa
- An kashe mutum 15 an yi garkuwa da 12 a Neja
Shugaban kungiyar ’yan kasuwar, Mustapha Shu’aibu Sulaiman ya bayyana wa manema labarai cewa motocinsu guda biyu da suka yi dakon manjan daga Jihar Akwa Ibom aka kone su kurmus.
Rahotanni sun ce banka wa motocin wuta ya janyo wa ’yan kasuwar tafka asarar dukiya ta kimanin N77m.
’Yan kasuwar sun zargi Gwamnatin Jihar Kano da nuna halin ko-in-kula game da halin da suka sami kansu ciki.
“Babu wani daga cikin mahukunta daga Jihar Kano da ya zo ya nuna alhini game da abin da ya same mu na iftila’in. Sai dai mune muke bai wa ’yan kasuwarmu hakuri,” inji Shugaban kungiyar.
’Yan kasuwar sun yi kira ga gwamnatoci a dukkanin matakai musamman na tarayya da su taimaka musu wajen biyan su diyyar barnar da aka yi musu.