✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Hausawa da Yarabawa: An kashe mutum 20 wasu 5,000 na gudun hijira

Mutum 3,000 na zaman gudun hijira a gidan Sarkin Hausawan Sasa

Akalla mamata 11 ne aka binne ranar Lahadi bayan rikicin da ya barke tsakanin al’ummar Hausawa da Yarabawa a Kasuwar Sasa da ke Karamar Hukumar Akinyele ta Jihar Oyo ya yi ajalin su.

Sakamakon rikicin, kimanin mutum 5,000 da suka hada da Hausawa ’yan tireda da mata da kuma kananan yara na zaman mafaka a gidan Sarkin Hausawan Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin da Cibiyar Binciken Tsirrai ta IITA da ke Ibadan.

Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin ya shaida wa Aminiya ta waya cewa sama da mutum 3,000 ke neman mafaka a gidansa; “Ga hayaniyarsu kana ji, har yanzu suna nan.”

Ya bayyana wa Aminiya cewa an yi jana’izar mutum 11 a gidan nasa yayin da wani mazaunin garin ya bayyana cewar an binne mutum 20 da aka kashe a Makabartar Akinyele da ke garin Ibadan.

Ya kara da cewa zuwa yammacin ranar Lahadi akwai karin gawarwaki takwas  hannun ’yan sanda.

Gwamna Seyi Makinde da Rotimi Akeredolu a lokacin ziyarar da suka kai wa yankin Sasa.

Wakilinmu ya fahimci cewa ana ci gaba da zama cikin zullumi a garin a yayin da ’yan kasuwa daga bangaren Hausawa da Yarabawa ke lissafin asarar da suka tafka a rikicin.

Musbbabin rikicin

Rikicin ya fara ne a ranar Alhamis bayan wani dan dako da ya dauko kayan tumatir ya ture wata Bayarabiya bisa kuskure.

Ana zargin bayan matar ta rama, daga baya ta kawo ’yan daba Yarabawa cewa su daukar mata fansa.

Daga nan rikicin ya ci gaba ranar Juma’a tare da sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da kona ka tuna da gidaje da kuma wuraren ibada.

Aminiya ta gano yadda al’ummar Hausawa a unguwar Mokola, ke ta taruwa a wuri guda saboda tsoron barkewar rikici a unguwar.

Mokola ita ce unguwar Hausawa mafi girma a garin Ibadan.

Wakilinmu ya ga an girke jami’an ’yan sanda a gidan Sarkin Hausawa da ke Mokola domin tabbatar da doka da oda a yankin Sabo.

An yi wa Gwamna ihu a  Shasa

A rana Lahadi fusatattun mazauna Shaida sun yi wa Gwamnan Jihar ta Oyo Seyi Makinde ihun nuna fushinsu a lokacin da shi da takwaransa na Jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu suka ziyarci yankin.

Mazaunan sun yi hakan ne saboda zargin Gwamna Makinde da jinkirin kawo musu ziyarar jaje.

Al’ummar Yarabawa sun kuma yi wa gwamnonin tirjiya suka hana shi ziyarar fadar Sarkin Hausawa na Sasa wanda suka zarga da rashin kwabar mabiyansa bayan ballewar rikicin a ranar Alhamis.

Hakan ta sa Makinde da Akeredolu takaita ziyarar tasu ga gidan baraken Yarabawan yankin, Baale.

Wani mazaunin yankin mai suna Hassan wanda ya ce an kashe abokansa da dama ya zargi Gwamna Makinde da mantawa da cewa al’ummar Hausawa ma sun zabe shi a 2019.

Yawancin mazauna da Aminiya ta sanya da sun shaida mata cewa an sanar da su cewa kar su doga da jam’an ’yan sanda domin samun kariya, gara su shirya su kare kawunansu daga harin ’yan daba.

Daga Sagir Kano Saleh,  Jeremiah Oke, Kabiyu Y. Ali (Ibadan), Muideen Olaniyi, Dalhatu M Liman (Abuja), Abdullateef Aliyu (Legas), Lami Sadiq (Kaduna) & Shehu Umar (Gusau)