✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yakin Gaza: Yadda ake kwaso ’yan Najeriya da suka makale

An kashe ’yan kasar Thailan 20 a yayin da Kasashe ke rububin kwashe ’yan kasarsu da suka makale a yankin Falasdinawa da Isra'ila

Najeriya ta kwaso ’yan kasarta sama da 300 da suka makale a yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin Isra’ila da mayakan Falasdinawa.

Najeriya ta kwashe su ne bayan da suka tsallaka zuwa kasar Jordan, daga Isra’ila inda suka kai ziyarar ibada daga Jihar Legas.

Ga yadda gwamnatoci ke kwashe ’yan kasashensu daga Isra’ila da yankin Falasdinawa:

An kwashe ’yan Najeriyar masu ziyarar ibada a Isra’ila ne a yayin da dubban ’yan kasashen waje suka makale a Isra’ila da Falasdinu sakamakon yakin bangarorin da ya shiga kwana da biyar.

Akalla mutum dubu uku ne suka rasu, wasu kimanin dubu hudu suka jikkata daga gangarorin biyu; lamarin da ya sa kasashe rububin kwashe ’yan kasashen da ke can zuwa gida.

1-Thailand

A safiyar Alhamis ’yan kasar Thaildan da suka makale a yakin suka isa birnin Bangok bayan an kwashe su. Hukumomin Thailand sun bayyana cewa ’yan kasar 21 sun rasu yakin da ke gudana tsakanin Isra’ila da Hamas.

2- Argentina
Tun ranar Talata Argentina, kasar Latin da ta fi yawan Yahudawa ta kwashe ’yan kasarta 1,246 daga Isra’ila a jiragen soji zuwa kasar Itlaliya  daga nan a mayar da su kasarsu, kamar yadda suka bukata a cewar ma’aikatar tsaron kasar.

3- Switzerland
Ita ma Switzerland a ranar ta kwashen ’yan kasarta 220, wadanda sahu na biyu mai mutum 215 ya biyo bayansu ranar Laraba, kafin ranar Alhamis a kwashi rukuni na uku mai mutum 215 daga cikin ’yan kasar 28,000 da ke Isra’ila da yankin Falasdinu.

4-Koriya ta Kudu
A safiyar Laraba jirgi dauke da ’yan kasar Koriya ta Kudu 192 da suka makale a Isra’ila ya sauka a birnin Seoul.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar ta ce kafin karewar mako za ta kwashe karin mutum 30 tare da wasu mutum 27 da suka hada da Isra’ilawa da masu ziyarar ibada da za su tsallaka zuwa kasar Jordan ta mota.

5-Portugal
Portugal ta kwashe ’yan kasarta 152 a safiyar Laraba a cikin jirgin soji, tare da wasu mutum 14 ’yan kasahen Turai.

6-Norway
Da yamma Norway ta tura jirgi domin kashe ’yan kasarta kusan 500 da suka makale a Isra’ila da yankin Falasdinawa.

7- Girka
A ranar Laraba Ma’aikatar Harkokin Wajen Girka ta ce ranar Laraba ta kwashe ’yan kasarta 90 daga Isra’ila, ranar Alhamsi kuma jirgi na biyu zo ya kwashi wasu.

8- Canada
Canada ta tura jirage biyu domin kwashe ’yan kasarta, kimanin 4,200 ne ke da rajista a Isra’ila da wasu 470 a yankunan a Falasdinawa, a cewar ministtar harkokin wajenta, Melanie Joly.

9- Brazil
Brazil ta ware jirage shida don kwashe ’yan kasar 14,000 da suka makale a Isra’ila da wasu 6,000 da ke yankin Gaza, inda ranar Laraba rukunin farko na mutum 211 suka tafi gida, rukuni na biyu kuma zai tashi ranar Alhamis.

10- Spain
A Labarar dai Spain ta kwashe rukunin farko na ’yan kasarta 185 da wasu ’yan kasashen Turai da kuma Latin su 24.

Jirgi na biyu zai tashi da mutum 220, ciki har da mutum 149 ’yan Spains.

11-Faransa
Ranar Alhamis jirage na musamman na Faransa za su isa Isra’ila domin kwashe ’yan kasarta da suka makale.

12-Jamus
Jamusu kuma Alhamis da Juma’a take sa ran kwashe nata ’yan kasar kusan 4,500 da ke neman komawa gida.

16- Ukraine
Jakadan Ukraine a Isra’ila, Yevgen Korniychuk ya ce  Laraba za a kwashe sahun farko daga Isra’ila, rukuni na biyu kuma daga baya.

Kimanin mutum 1,ooo ’yan Ukraine ne suka nemi a mayar da su gida daga Zirin Gaza da sauran sassan Isra’ila kuma kullum adadin karuwa yake.

sai dai jakadan ya ce za a kai su kasashen makwabta irin su Moldova, Romania, Slovakia da Poland, ne saboda mamayar da Rasha ta yi a kasar, wanda ba zai ba da damar mayar da su gida kai-tsaye ba.

17-Iceland
Gwamnatin Iceland ta sanar cewa za ta tura jirgi domin kwashe ’yan kasarta kusan 120 da suka makale a Isra’ila.