Babban Malamin Musuluncin nan kuma Jagoran Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi Usman Bauchi ya ba da gudunmawar Naira miliyan 100 domin tallafa wa mutanen Faladinu da Isra’ila ke yi mata yakin mamaya.
Sheikh Dahiru Bauchi ya ba da gudunmawar ce lokacin da aka karanta masa wasikar da Halifan Sheikh Ibrahim Nyass, Khalifa Sheikh Muhammadul Mahy Inyass ya rubuta wa dukkan almajiran Shehu Ibrahim cewa su taimaka a tara Dala miliyan daya da ya ce za a bai wa Falasdinawa da yaki ya tagayyara.
- An kafa dokar hana fita bayan harin barikin soji da fasa gidan yari a Saliyo
- Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, Isra’ila ta kashe Falasdinawa 8
Takardar wadda Kakakin Shehu Mahiy a Nijeriya, Sayyadi Ibrahim Dahiru Bauchi ya kawo, an umurce shi ya hada kan dukkan almajiran Shehu Ibrahim su taimaka a hada wannan kudi.
Da yake kaddamar da asusun, Sheikh Dahiru Bauchi ya ba da gudunmawar Naira miliyan 100, inda ya bukaci jama’a su cika saura Naira miliyan 900 da ya rage.
Shehin ya ce, kada gwiwar kowa ta yi sanyi, kowa ya yi iyakacin kokarinsa don ganin ya ba da gudunmawa don a tara wannan kudi.
Da yake karin haske, Sayyadi Ibrahim Dahiru Bauchi ya ce, akalla kowane almajirin Shehu Ibrahim ya kamata ya ba da Dalar Amurka daya kwatankwacin Naira 1,200.
Sai ya yi kira ga dukkan Musulmi, musamman ’yan Tijjaniyya su yi kokarin bayar da nasu taimakon ta asusun banki na: SHEIKUL ISLAM ALHAJI IBRAHIM INYASS FOUNDATION, 0125407863 a WEMA BANK.
Sayyadi Ibrahim ya ce, abin da ya kawo wannan magana shi ne, Shehu Mahiy ya halarci taro ne a kasar Mauritaniya, inda aka fayyace halin da Falasdinawa suke ciki, sai ya yi alkawarin almajiran Shehu Ibrahim za su tallafa da Dalar Amurka miliyan daya sama da Naira miliyan dubu.