✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Gaza: Masar ta tura motoci su kwaso Falasdinawa

Masar za ta bude iyakar da nufin ba wa wanda suka ji rauni agajin gaggawa.

Masar ta bude iyakarta, ta kuma aike da motocin daukar marasa lafiya su kwaso Falasdinawa da hare-haren Isra’ila suka jikkata a Zirin Gaza.

Hukumomin Masar sun bude iyakarta ta Rafah da ke iyaka da Gaza ne a ranar Asabar da nufin agaza wa Falasdinawa da hare-haren Isra’ila ke ci gaba da ragargaza muhallansu a Gaza.

Masar ba ta bude iyakar Rafah sai a ranakun aiki, amma ta jingine hutun Karamar Sallah ta bude ta don kwaso Falasdinawan domin a yi jinyar su a asibitocin kasarta.

An soke hutun likitoci don kai agaji Gaza

Tun a ranar Juma’a Hukumar Lafiya ta Masar, ta dakatar da hutun likitoci na Karamar Sallah, a yunkurinta na agaza wa Falasdinawan da hare-haren Isra’ila suka jikkata a Gaza.

epa08597371 A Palestinian Ambulance crosses into Egypt through the Rafah border crossing between Gaza Strip and Egypt after five months of closure as a precautionary measure against the spreading of the coronavirus disease (COVID-19) pandemic, in Rafah, southern Gaza Strip, 11 August 2020. Egyptian Authorities reopened Rafah crossing for three days for humanitarian cases, including allowance of crossing the border of people needing medical treatment unavailable in Gaza as well as students enrolled at Egyptian universities and Gazans with jobs abroad. EPA-EFE/MOHAMMED SABER

‘Barnar ta yi yawa’

Jami’an lafiya a Gaza sun ce hare-haren saman Isra’ila a Gaza sun kashe Falasdinawa 145 ciki har da yara 41, wasu mutum 1,100 kuma sun ji rauni.

Rokokin da Falasdinawa suka harba kuma sun kashe Yahudawa 10, ciki har yaro karami da wani soja, wasu mutum 560 suka ji rauni a Isra’ila.

Abin da ya faru

Isra’ila ta shafe kwanaki tana amfani da daruruwan jirage da tankokin yaki da bindigogin atilare tan kai hare-hare a yankunan Falasdinawa a Zirin Gaza.

Fadan na wata Mayu ya samo asali ne bayan ’yan sandan Isra’ila sun  kutsa cikin masallacin Kudus suka rika duka da kamen Falasdinawa da ke zanga-zanga a harabar masallacin kan shirin Isra’ila na mamaye unguwanninsu da ke gabashin Gaza.

Bayan matakin da ya sha la’anta daga sassan duniya ne, kungiyar Hamas ta ba da wa’adin janyewar dakarun Isra’ila da janye yunkurin.

Cikar wa’adin ke da wuya, Hamas da kungiyar Jihadin Islama suka shiga yi wa Isra’ila ruwan rokoki na tsawon akalla kwana biyar.

Rundunar Tsaron Isra’ila (IDF) ta ce kawo yanzu sama da rokoki 2,000 ne aka harba a kan Isra’ila.

Ministan Harkokin Wajen Masar, Sameh Shoukry ya tattauna da takwaransa na Saudiyya inda ya bukaci da a tsagaita da wuta haka.

Limaman Azhar da Cocin Coptic sun la’anci Isra’ila

A ranar Juma’ar babban limamin masallacin Jami’ar Al-Azhar, Sheikh Ahmed al-Tayeb, ya kaddamar da gangamin la’antar Isra’ila a kafafen sada zumunta da taken “A taimaki Falasdinawa”.

Sheikh Tayeb ya ce, “Shiru da kuma tufka da warwara da muke yi sun isa haka, idan har da gaske muke maganar wanzar da zaman lafiya.”

Shi ma daga bangarensa, Shugaban Cocin Coptic, Fafaroma Tawadros, ya soki yadda hare-haren Isra’ila suka yi sanadiyyar rasa rayukan daruruwan mutane a birnin Kudu da kuma Gaza.