Shugaban Kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi da Sarki Abdallah II na Jordan sun Bukaci a tsagita wuta a rikicin Falasdinawa da Isra’ila.
Shugabannin kasashen Labawan sun yi kira ne a tattaunarsu da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa kan yadda za a tabbatar da ganin kurar ta lafa.
“Babbar manufar tattaunawar shugabannin uku ita ce samo mafita cikin sauri na ganin an dakatar da musayar wuta da kuma hana ci gaban rikicin,” inji Fadar Elysee ta Faransa.
Sisi ya yi amfani da damar halartar taron kasashen Afirka daga ke gudana a birnin Paris na Faransa wurin halartar tattaunawar wadda Sarki Abdallah Jordan ya halarta ta bidiyo.
Mako na biyu ke nan ana ragargazar juna da bama-bamai tsakanin kungiyar Falasdinawa ta Hamas da kasar Isra’ila.
Isra’ila ta yi amfani da daruruwan jiragen yaki da jirage marasa matuki da tankoki da bindigogin atilare wajen kai hare-hare a yankunan Larabawan Falasdinawa da ke Gabashin Zirin Gaza.
A martaninta, kungiyar Hamas ta harba wa Isra’ila sama da rokoki 2,000 a rikicin da ya samo asali daga shirin Isra’ila na mamaye matsugunan Falasdinawa a Gabashin Gaza.
Yunkurin na Isra’ila a cikin watan Ramadan ya sa Falasdinawa gudanar da zanga-zanga a daura da Masallacin Kudus.
Sakamakon haka, ’yan sandan Isra’ila suka kai samame a kan masu Sallar Tahajjud a cikin harabar masallacin, suka rika harba hayaki mai sanya hawaye.