Mutane da dama sun rasu a wani sabon rikici tsakanin Fulani makiyaya da ’yan kabilar Kutep a Karamar Hukumar Ussa ta Jihar Taraba.
Duk da cewa ba a kai ga gano musabbabin sabon rikicin ba, amma wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa ’yan Kutep na zargin Fulani makiyaya da yin garkuwa da ’yan kabilar.
- Gwamnatin Kano ta ba wa Kamfanin Triumph shaguna 64 a Kasuwar Canjin Kudi
- Yadda sojoji suka ragargaji ISWAP da Boko Haram A Borno
Hakan ne ya yi sanadin kai wa wasu makiyaya hari a yankin Kwe, har rikicin ya watsu zuwa garin Fikye, inda aka kashe mutane da dama.
Shugaban Kungiyar ’Yan Kabilar Kutep na Kasa, Emmanuel Ukwen, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa rikicin ya yi ajalin mutane da dama baya ga gidajen da aka kona a kowane bangare kuma kurar ba ta lafa ba.
Aminiya ta gano cewa wasu fusattun matasa sun kai hari tare da kona fadar basaraken Lisam Kwe, Ando Madugu, kan zargin sa da goyon bayan Fulani makiyaya.
Shugaban Karamar Hukumar Ussa, Abershi Musa, ya yi murabus daga mukaminsa bisa zargin gwamnatin jihar da gaza daukar mataki kan kashe-kashen da ya ce makiyaya suke yi a yankin.
A yayin hada wannan rahoton, wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, amma hakan bai samu ba.
Ya kuma tuntubi shugaban kungiyar makiyaya ta Miyyetti Allah (MACBAN) ta kasa reshen Karamar Hukumar Ussa, Alhaji Bello, amma ya ce sai daga baya zai yi bayani.