Mahara sun kone gidaje akalla 96 a yankin Gyenbwas na gundumar Langai da ke karamar hukumar Mangu a jihar Filato.
Mazauna yankin sun kuma yi zargin cewa maharan sun kuma kwashe musu kayan abinci da katifu da kuma shanu da sauran kayayyaki.
Alhaji Yakubu Umar, wanda kuma shi ne Madugun Langai ne ya shaida wa Aminiya hakan a ranar Talata.
- A hanzarta kwangilar yashe Madatsar Ruwa ta Alau — Gwamnatin Borno
- Saudiyya za ta fara bayar da bizar Umara
Ya kuma ce bayan mutum biyun da aka kashe musu ranar Litinin, sun kuma kara samo gawar mutum daya a yankin, wanda hakan ya kai adadin mutanen da aka kashe yayin harin zuwa uku.
Mazauna yankin dai na zargin ’yan kabilar Birom da kai musu harin, kodayake su kuma sun musanta hakan.
A cewar Alhaji Yakubu, “Ba a taba yi mana irin wannan ta’addancin ba. maharan sun kone kayan amfani masu yawa ciki har da sutturu da kuma kayan abinci. Sannan sun sace kayayyakinmu na miliyoyin naira. Mu a gaskiya muna zaune da kowa lafiya a nan, shi ya sa ma harin ya yi matukar daure mana kai.
Daga nan sai ya yi kira da gwamnati da ta binciki harin domin ta hukunta wadanda ke da hannu a ciki sannan ta kai wa wadanda suka yi asara tallafi.
Ba mu muka kai harin ba – Birom
Sai dai Kungiyar Matasa Birom (BYM) ta karyata labarin kai harin, inda ta bayyana shi a matsayin na kanzon kurege.
Shugaban kungiyar, Dalyop Solomon, ya ce, “Jiya akwai mambobinmu uku da aka kai wa hari yayin da suke aiki a gonakinsu, wadanda yanzu haka suna asibiti ana kula da su. Abin da muka sani kawai shi ne mutanenmu na cikin fargaba, kawai Fulani na fitowa ne saboda su samu dalilin kai mana hari.
“Amma ya kamata su sani, duk lokacin da suka kai mana hari, muna da ’yancin kare kanmu. Ba mamaki abin da ya faru ke nan. An zo kawo musu hari suka fatattaki maharan har zuwa maboyarsu, amma mu ba mu taba kai wa Fulani wani hari ba,” in ji Dalyop.