✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin #EndSARS: Makarantun Abuja na tura dalibai gida

Kasa da mako guda da bude makarantu a Birnin Tarayya bayan kullen COVID-19, makarantu sun fara tura dalibai gida sakamakon rikicin da ke barkewa da…

Kasa da mako guda da bude makarantu a Birnin Tarayya bayan kullen COVID-19, makarantu sun fara tura dalibai gida sakamakon rikicin da ke barkewa da masu zanga-zangar #EndSARS da ke ci gaba.

Makarantu na fargabar dauki ba dadin na iya rura wutar rikici shi ya sa suka dauki matakin.

Makarantar Destiny Christian Academy ta aike wa iyayen dalibai cewa, “Sakamakon rikicin da zanga-zangar da ke gudana a Abuja inda aka rufe wasu hanyoyi, bayanan da muke samu na bukatar lura da yanayin sosai a ranar Alhamis da Juma’a da ma gaba da haka.

“Bayan zaman hukumar gudanarwa, muna sanar da ku rufe makarantun (firamre da sakandare) nan take yayin da za mu ci gaba da sa lura da abin da ke faruwa sannan mu sanar da ku game da bude makarantun a ranar Litinin 19 ga Oktoba, 2020…”

Idan ba a manta ba wani sako da ya karade kafafen zumunta da ke cewa “…muna lura da rahotannin zanga-zangar EndSARS da aka shirya a Lugbe da Airport Road inda masu zanga-zanga za su taru a Shoprite Mall, Lugbe da karfe 8 na safe.

“Ana sa ran hakan zai shafi zirga-zirgar ababen hawa don haka ake bukatar jama’a su sauya hanaya, su rika lura, sannan su nesanci taron mutane da yawa”.