Rikici kan daukar sabbin kuratan ’yan sanda 10,000 a Najeriya ya kara munana a yayin da ma’aikatan Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda (PSC) ke shirin fara yajin aikin sai bana ta gani.
Ma’aikatan Hukumar za su fara yakin aikin sai abin da hali ya yi daga ranar Litinin, 29 ga watan Agusta da muke ciki bisa zargin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da yunkurin kwace aikin daukar sabbin ’yan sandan daga hannun hukumarsu.
- Abubuwan da ya kamata ku sani a kan ranar Hausa ta Duniya
- NAJERIYA A YAU: Ranar Hausa Ta Duniya: Yadda Harshen Uwa Zai Taimaka Wurin Inganta Ilimi
Suna kuma zargin hukumar gudanarwar PSC da rashin yi musu karin girma da kuma kin tura su zuwa kwasa-kwasai na samun horo.
Rikicin PSC da Rundunar ’Yan Sanda
Wannan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ke tsaka da yin ja-in-ja da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya kan wanda ke da alhakin daukar sabbin kuratan ’yan sanda 10,000 da Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarni.
A makon jiya ne Hukumar Kula da Aikin Dan Sandar (PSC) ta fitar sanarwa a jaridu cewa za ta fara daukar kananan ’yan sanda.
Bayan haka ne Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya fitar da tasa sanarwar tare da gargadin ’yan Najeriya su yi watsi da sanarwar ta PSC.
Rikicin cikin gida a Hukumar PSC
Don haka ta ce, an kai su makura, ba za su hakura ba, kuma daga ranar Litinin mambobinta za su tsunduma yajin aiki sai abin da hali ya yi.
A cewarta, babu abin da zai sa su mayar da wukarsu cikin kube face a biya musu bukatunsu da aka cim-ma yarjejeniya a kai.
Wasikar da gamayyar kungiyoyin ma’aikatan ta aika wa shugaban hukumar, tsohon Shugaban ’Yan Sandan Najeriya Musiliu Smith, ta ce za su shiga yajin aikin ne saboda an ki biya musu bukatunsu, tun bayan da suka janye yajin aikin gargadi na kwana uku da suka fara ranar 24 ga watan Janairu, 2022.
“Muna fada da babbar murya cewa hukumar gudanarwar PSC ta ki yin duk abin da zai kawo dorewar fahimtar juna da kyakkyawan yanayin aiki ba.
“Saboda haka za mu ci gaba da gwagwarmaya har sai hakarmu ta cim-ma ruwa — an aiwatar da duk alkawura da muka yi yarjejeniya a kansu.
“A bisa haka ne kungiyar da daukacin ma’aikatan hukumar ke sanar da cewa za su fara yajin aiki sai abin da hali ya yi daga ranar Litinin 29 ga watan Agusta, 2022.”
Wasikar da wakilinmu ya samu ganin kwafinta na dauke da sa hannun Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Ma’aikata Reshen PSC, Adoyi Adoyi; Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Gwamnati (NCSU), Abayomi Anthony; Sakataren Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati (ASCSN), Yusuf Nasidi da kuma Sakataren NCSU, Remi Ogundeji.
Hakamu ta yi na jin ta bakin Shugaban Hukumar PSC, tsohon Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Musiliu Smith, ba ta cim-ma ruwa ba; Mun kira wayarsa, amma ba ta shiga.