✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Rikicin Boko Haram ya gurgunta ’yan tumatir a Bauchi’

Alhaji Sani Abubakar shi ne shugaban kungiyar ’yan tumatir ta kasa reshen Jihar Bauchi. Ya tattauna da Wakilinmu a ofishinsa da ke kasuwar Muda Lawal,…

Alhaji Sani Abubakar shi ne shugaban kungiyar ’yan tumatir ta kasa reshen Jihar Bauchi. Ya tattauna da Wakilinmu a ofishinsa da ke kasuwar Muda Lawal, inda ya yi tsokaci game da matsalolin da kungiyar take fuskanta da kuma nasarorin da ta cimma.  Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Yaya kuke gudanar da harkokinku?
Alhaji Sani: Gaskiya a yanzu abubuwa sun tsaya cak sakamakon tashe-tashen hankula a shiyyar Arewa maso Gabas. A baya mukan je jihohin Borno da Yobe da Adamawa domin yin fataucin kayayyakin gwari, wadanda suka kunshi tumatir da albasa da attarugu da sauransu. Amma yanzu babu hali, domin akwai wasu daga cikin abokan kasuwancinmu wanda aka kashe su, misali, yanzu haka daga Bauchi sai mun je Zariya ko Sakkwato domin sayo wadannan kayayyaki, akwai dimbin mutane da suke son zuwa Jihar Borno domin sayo kayan gwari, amma kowa yana tsoro. A gaskiya ya kamata gwamnatin tarayya ta sake damara game da yadda take tafiyar da harkokin tsaro a kasar nan.
Tun lokacin da na karbi ragamar shugabancin wannan kungiya babban abin da nasa a gaba shi ne, yadda zan bunkasa harkokin kungiya. Kuma an samu gagarumin canji domin da yawa daga cikin mambobin wannan kungiya mutane ne masu hankali da hangen nesa. Sai dai ka san duk inda ka tara mutane dole ka samu nagari da na banza.
Abin farin cikin shi ne mambobinmu sun san dokokin kungiya kuma muna iya bakin kokarinmu domin yin adalci ga kowa da kowa, kuma wanda ya taka doka mukan hukunta shi daidai laifinsa.
Aminiya: Wadanne nasarori kungiyarku ta cimma a halin yanzu?
Alhaji Sani: Tabbas kungiyarmu ba ta rasa wasu kananan matsaloli, sai dai kuma lokacin da na karbi ragamar shugabancin kungiyar abubuwa sun fara daidaita. Na samu kungiyar ba ta da ofis a cikin wannan kasuwa, amma cikin kankanen lokaci sai ga shi mun gina babban ofis a cikin wannan kasuwa ta ’yan gwari. Ka ga wannan babbar nasara ce. Kai tsaye duk lokacin da wani bako ya zo ya san ofishin kungiya, kuma duk lokacin da ka zo kasuwar za ka samu dimbin mutane kowa yana hada-hadarsa. Mun inganta yanayin cinikayya tsakanin masu saya da masu sayarwa.
Aminiya: Batun matsaloli fa?
Alhaji Sani: Tashin hankalin da ke faruwa a wasu jihohin Najeriya ya gurgunta ’yan tumatir fiye da tunanin mutune. Saboda haka muna fata Allah Ya zaunar da Najeriya lafiya, domin ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya.
Aminiya: Mene ne sakonka ga mambobin wannan kungiya ta ’yan tumatir?
Alhaji Sani: Babban sakona ga mambobin wannan kungiya ta ’yan gwari shi ne, ya kamata mu zamo mutane masu gaskiya da rikon amana tare da yin hakuri da abokan kasuwancinmu, domin Hausawa sun ce zo mu zauna, zo mu saba. Ina gode wa ’yan kungiya saboda goyon bayan da suke ba ni.