✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin APC: Tsagin Shekarau zai daukaka kara bayan hukuncin Kotu

Ganduje ya ce hukuncin zai kara hada kan jam'iyyar APC a Jihar Kano.

Tsagin jam’iyyar APC a Jihar Kano da ke rikici da na Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce zai daukaka kara kan hukuncin kotu da ya ce shugabancin bangaren gwamna ne halastacce.

Shugaban tsagin, Ahmadu Haruna Zago, wanda ke samun goyon bayan tsohon Gwamna Sanata Ibrahim Shekarau, ya fada wa BBC Hausa cewa za su yi biyayya ga hukuncin amma za su daukaka kara.

“Za mu daukaka kara mana, ai bin umarnin daban kuma daukaka kara daban,” in ji shi.

“A halin yanzu Lauyoyinmu na nazari kan hukuncin kotun.”

Hakan na nufin Kotun Koli ce za ta raba gardama idan suka daukaka karar, kasancewar Kotun Daukaka Kara ce ta yi hukuncin na yanzu.

Aminiya ta ruwaito cewa, a zaman da ta yi ranar Alhamis a Abuja, Kotun Daukaka Kara ta ce Babbar Kotun Abuja ba ta da hurumin yin hukunci kan rikicin sannan kuma ta ce shugabancin Abdullahi Abbas ne halastacce – ba na Haruna Zago ba.

A makon da ya gabata ne tsagin Shekarau ya yi watsi da wani yunkurin sulhu da jam’iyyar ta kasa ta yi, inda ta nada Gwamna Ganduje a matsayin jagoran kwamitin sasanta rikicin da suke yi.

Hukuncin da Kotun ta zartar zai kara hada kawunanmu —Ganduje

Sa’o’i kadan bayan hukuncin da Kotun Daukaka Karar ta zartar, Gwamna Abdullahi Ganduje ya nemi tsagin na tsohon Gwamnan Jihar da ya zo a hada hannu domin ciyar da jam’iyyar APC gaba a Jihar Kano.

Da yake martani kan hukuncin da kotun ta zartar, Gwamnan ya ce tun gabanin soma shari’ar ba ya da wani shakku a kai domin kuwa yana da tabbacin cewa kotun za ta yi abin da ya dace, kuma a yanzu yana farin ciki da hakan.

Gwamnan wanda ya yi wannan furuci ta bakin Kwamishinan Labarai na Jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya ce hukuncin da kotun ta zartar zai kara bunkasa hadin kai da daidaito a jam’iyyar APC reshen Jihar Kano.

A kan haka ne yake cewa yana fatan bangaren Shekarau zai karbi hukuncin da kotun ta zartar a matsayin kaddara ta dawowa a hadu kai da fata domin fasalta jam’iyyar APC a kan turbar da za ta kai kan tudun mun tsira a Zaben 2023 da ke tafe.