✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin APC: Ganduje ya kayar da Shekarau a Kotun Daukaka Kara

Kotun daukaka kara ta ce kotun da ta ba wa bangaren Shekarau nasara ba ta da hurumi.

Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta ba bangaren Sanata Ibrahim Shekarau nasara a kan rikicin shugabancin jam’iyyar APC a Jihar Kano.

A safiyar Alhamis Kotun Daukaka Karar ta jingine hukuncin bisa hujjar cewa babbar kotun ba ta da hurumin suraron shari’ar.

A baya dai kotun tarayyar ta yanke hukuncin rushe zaben mazabu da kananan hukumomi na bangaren Gwamna Ganduje.

Amma a zaman Kotun Daukaka Kara a ranar Alhamis ta jingine wancan hukuncin bisa dalilin cewa kotun baya bata da hurumi.

Kotun ta bayyana cewa abin da ya kai bangarorin gaban kotu rikici ne na cikin gida da uwar jam’iyyar APC ke da alhakin daidaitawa.