✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikici: ’Yan sanda sun kashe matasa 2 a Kano

'Yan sandan sun tsere daga wajen bayan ganin yadda lamarin ya rincabe.

Ana zargin ’yan sanda sun harbe tare da daba wa wani matashi Abubakar Isah mai inkiyar Banupe da Ibrahim Sulaiman mai inkiyar Mainasara wuka a unguwar Sharada da ke garin Kano a daren Asabar.

Wani wanda ya gane wa idonsa faruwar lamarin Sahabi Yusha’u, ya shaida wa Aminiya cewa abun ya faru ne da misalin karfe 11 na dare a daidai masallacin Juma’a na Unguwar Sharada wajen cin taliyar yara.

“An samu tirjiya daga wajen abokan wanda ‘yan sanda masu yaki da ayyukan ‘yan daba suka zo kama wa.

“A wannan lokacin ne daya daga cikin ‘yan sanda ya daba wa Ibrahim Sulaiman Mainasara wuka sau biyu.

“Nan take hargitsi ya kaure tsakanin ‘yan sanda da matasan wajen sai suka bude wuta wanda a nan ne harsashi ya samu Abubakar Isah Banupe, nan take rai ya yi halinsa, in ji Yusha’u.

Ibrahim Sulaiman Mainasara da Abubakar Isah Banupe

Ya ce “an dauke su zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad domin basu agajin gaggawa, amma daga bisani shi ma Mainasara ya rasu.”

“Haka ya sanya ‘yan sandan suka tsere daga wajen bayan ganin yadda lamarin ya rincabe.”

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin jami’in hulda da al’umma na rundunar ‘yan sandan jihar Abullahi Haruna Kiyawa, sai dai bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.