Wani sabon rikici ya kunno kai a kan zabin dan takarar mataimakin shugaban kasa a Jam’iyyar PDP.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, ke kara tuntubar masu ruwa da tsaki.
- Dansarauniya ya nemi afuwar Ganduje kan bata masa suna a Facebook
- Alarammomin Kano sun gudanar da addu’o’i na musamman don samun tsaro da shugaba na gari
Wani sabon rikici ya kunno kai a kan zabin dan takarar mataimakin shugaban kasa a Jam’iyyar PDP.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, ke kara tuntubar masu ruwa da tsaki.
An ruwaito Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, yana barazanar ficewa daga PDP muddin Atiku ya zabi Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.
Wike ya yi barazanar ne bayan an gabatar da sunan Okowa a cikin mutanen da ake so su yi takara tare da Atiku, a lokacin taron da tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya yi da gwamnonin jam’iyyar a kan zabin wanda zai tsaya tare da shi.
A ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki da Atiku Abubakar yake yi, zai gana da tsofaffin gwamnoni da ministocin jam’iyyar a karshen makon nan a Abuja.
Ko a ranar Laraba, dan takarar ya yi irin wannan zama da gwamnonin PDP.
Wata majiya mai masaniya game da zaman da za a yi a karshen mako ta ce hakan wani bangare ne na kokarin dan takarar na “daidaita bukatun dukkan sassan jam’iyyar kafin ya kai ga zabo mataimakin nasa.”
Majiyar ta ce a taronsa da su, gwamnonin sun nemi ya zabi daya daga cikinsu, ciki har da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, wanda ya zo na biyu a zaben fid-da-gwani.
Adawa da Okowa
Sauran su ne Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, da Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, da Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri.
Majiyar ta ce: “Dan takarar mutum ne mai kaifin hankali kuma zai so mutumin da PDP za ta iya lashe zabe da shi.
“Dole ne ya yi tunanin mutumin da ya fahimci tattalin arziki na zamani saboda mummunan halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki, tare da daidaita muradun yanki da siyasa. Mun kuma san cewa lokaci yana neman kurewa.”
Kakakin Atiku, Mazi Paul Ibe, ya tabbatar da shirin dan takarar na ganawa da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.
“Haka ne, ana ci gaba da tuntubar juna kuma [Atiku] ya shirya tarurruka da dama a karshen mako, tare da tuntubar jam’iyya domin gabatar da abokin takara wanda ’yan Nijeriya za su so su zaba.”
Baya ga Gwamna Wike na Jihar Ribas, wata majiya ta ce shi ma tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori, yana cikin shugabannin jam’iyyar wadanda suke adawa da zabin Gwamna Okowa a matsayin abokin takarar Atiku.
Akwai kuma mutanen da aka ce daga cikinsu Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP yake so dan takarar ya dauki abokin takararsa.
Wadanda ake tunanin dauka
Mutanen sun hada da tsohuwar Ministar Kudi kuma Darakta-Janar ta Kungiyar Ciniki ta Duniya (WTO), Dokta Ngozi Okonjo-Iweala, da tsohon Shugaban Riko na Majalisar Wakilai, Emeka Ihedioha, da kuma tsohon Gwamnan Jihar Delta, Emmanuel Uduaghan.
Zabin abokin Takara dai na taka muhimmiyar rawa wajen samun nasara a zaben shugaban kasa.
Wasu masu sharhi ma suna ganin daya daga cikin dalilan da suka hana Atiku lashe zaben 2019 shi ne zabo Peter Obi da ya yi a matsayin abokin takararsa.
Wasu manazarta na ganin cewa ko ma wa Atiku ya dauka mutanen yankin Kudu maso Gabas za su zabi PDP, don haka da ya dauko dan wani yankin zai fi tasiri.
Daya daga cikin kalubalen da ’yan takarar manyan jam’iyyun Najeriya ke fuskanta a yanzu shi ne na zabo wanda zai taimaka musu cin zabe a cikin dan lokacin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ba su na mako guda.