An ba hamata iska tsakanin jami’an hukumar KAROTA da direbobin baburan A Daidaita Sahu a kusa da Kokar Nassarawa da ke Kano.
Rikicin da ya yi sanadiyyar jikkata mutane biyu, tare da fasinjojin baburan da sauran mutane yin yi cirko-cirko.
- Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar dakarunta a harin ’yan bindiga a Neja
- Abubuwan da suka hana Najeriya gyaruwa
Ana cikin haka ne kuma ’yan daba suka fara cin karensu babu babbaka, lamarin da ya sa mutane suka ranta a na kare domin tsira.
Shaidu sun ce rikicin ya samo asali ne bayan wasu ’yan KAROTA sun finciko wani direban A Daidaita Sahu kan saba doka kuma ya ki tsayawa, inda a garin haka, fasinjansa ya samu rauni, babur din kuma ya lalace.
Wani ganau mai suna Sani ya ce, “’yan KAROTA sun bukaci dan A Daidaita Sahun ya tsaya, amma ya ci gaba da tafiya, shi ne su ’yan KAROTA suka janyo babur din, a sakamakon haka duk suka fadi babur din ya lalace, fasinjansa kuma ya samu rauni a kafada, ina jin ma karaya ce.”
Bayan nan ne ’yan A Daidaita Sahu suka yi dafifi a ofishin KAROTA da ke kusa da wurin, wanda da baya abin ya koma rikici tsakanin bangarorin.
“Masu baburan suka rika ajiye fasinjojinsu a wurin, suka tafi goyon bayan wa abokin sana’arsu; a karshe dai sai da ’yan sanda suka suka kwantar da kurar,” in ji Sani.
’Yan KAROTA da masu A Daidaita Sahu dai sun jima suna wa juna kallon hadarin kaji a Kano, kan zargin jami’an hukumar da gallaza musu.
Daga baya Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauya shugabannin hukumar a wani yunkuri na kyautata alaka tsakanin bangarorin.
Mai magana da yawun hukumar KAROTA, Nabilusi Abubakar Kofar Naisa ya tabbatar da faruwar rikicin, inda ya ce ’yan sanda sun fara gudanar da bincike a kai.
“Muna da labarin rikici tsakanin masu A Daidaita Sahu da jami’an hukumarmu ta KAROTA a yau. Mun sanar da ’yan sanda kuma sun shawo kan lamarin.
“Idan suka kammala bincike za su sanar da jama’a kuma idan muka samu jami’anmu da laifi za mu hukunta su.
“Idan kuma masu baburan ne da laifi, su ma za a hukunta su, domin ya zama darasi nan gaba,” in ji shi.