✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar dakarunta a harin ’yan bindiga a Neja

Laftanar Lagbaja ya koma sansanin da abin ya shafa domin karfafa wa sojojin gwiwa a Neja.

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta tabbatar da mutuwar dakarunta a wani harin kwantan bauna da wasu ‘yan bindiga suka kai wa sansanin sojinta a Karamar Hukumar Wushishi da ke Jihar Neja.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya katse rangadin aikin da yake yi a Arewa-maso-Yamma, inda ya nufi Jihar Neja domin karfafa gwiwar sojojin.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce dakarun sun fafata da ’yan bindigar da suka yi musu kwanton bauna, amma wasunsu sun mutu a bakin fama.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa jirgin mai saukar ungulu na NAF MI-17, wanda ya yi hadari da yammacin ranar Litinin a kusa da kauyen Chukuba da ke Jihar Neja, yana dauke da sojoji da suka samu raunuka zuwa asibiti kafin aukuwar hadarin.

Ya kara da cewa “babban hafsan sojin kasa, Laftanar Lagbaja, yana rangadin gudanar da ayyuka a yankin Arewa maso Yamma lokacin da lamarin ya faru.

Ya ce “saboda haka Laftanar Lagbaja ya koma sansanin da abin ya shafa domin karfafa wa sojojin gwiwa, inda ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su karfafi gwiwar iyalan sojojin da abin ya shafa.”

A bayan nan ne dai shafukan sada zumunta suka cika da hotuna da bidiyoyi masu sosa zuciya na sojojin da ’yan bindigar suka kashe a karshen mako.

Wasu bayanai sun ce sojoji fiye da 2o sun mutu, cikinsu har da manyan sojoji uku, da ’yan bijilanti na JTF guda uku yayin da sojoji takwas suka jikkata a fafatawa mai zafi da aka yi a babban titin Zungeru zuwa Tegina.