✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikici ya barke tsakanin shugaban APC na Jihar Kano da jami’an tsaro a taron APC

Hatsaniyar ta tashi ne kan zargin magudi a yayin da daliget suke jefa kuri'a

An dakatar da jefa kuri’a a zaben fid-da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC bayan barkewar wata takaddama tsakanin shugaban jam’iyyar na Jihar Kano, Abdullahi Abbas da jami’an tsaro a zauren taron.

Hatsaniyar ta tashi ne kan zargin magudi a yayin da daliget suke jefa kuri’a a zauren taron da ke gudana a Abuja.

Daga baya kwamitin gudanar da zaben fitar da dan takarar ya shawo kan rikcin.

Sai dai kuma ya umarci duk wasu jami’an jam’iyyar da ke sanye da shudin riga su bar wurin da aka ware domin jefa kuri’a.

Daga bisani aka ci gaba da jefa kuri’a da aka fara da daliget din Jihar Legas tun da misalin karfe 2 na dare.

Jihar Kano na da daliget 127 da suka jefa kuri’a a zaben da ke gudana a safiyar ranar Laraba.