A Talatar makon da ya gabata ne aka samu labarin wani kazamin fada da aka fafata tsakanin wadansu manyan ’yan bindiga wato Dogo Gide da Damina, inda aka kashe Damina da aka ce ya dade yana addabar mutanen Jihar Zamfara.
Ana zargin Damina ya dade yana addabar mutanen Zamfara da hare-hare da satar mutane da shanu da tilasta wa mutane biyan haraji kafin su girbi gonakinsu musamman a yankin Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru a Jihar.
- Sarkin Musulmi ya cika shekara 15 a kan mulki
- PSG za ta raba gari da Ramos, Tottenham za ta dauki Conte
A watan Yulin da ya gabata, an yi zargin Damina da kai hari a garuruwan Tungar Baushe da Randa, inda aka ya kashe mutane da dama sannan ya yi garkuwa da kimanin mutum 100, yawancinsu mata da kananan yara.
Shi kuwa Dogo Gide, wanda aka ce ya kashe Damina, fitaccen dan bindiga ne a yankin, wanda a shekarar 2017 ya jagoranci kashe fitaccen dan bindigar wancan lokacin Buharin Daji wanda ubangidansa ne a garin Dansadau.
Rahotanni sun ce Damina ya rasu ne sakamakon raunukan da ya ji a musayar wuta a tsakanin yaransa da na Dogo Giden a kusa da kauyukan Chillin da Fammaje da suka karkashin ikonsa.
Wasu majiyoyi a yankin sun bayyanawa wa wakilinmu cewa Dogo Gide wanda ake da yakinin yana da alaka da Boko Haram bangaren ISWAP ba ya jin dadin yadda Damina yake gudanar da harkokin ta’addancinsa a yankin.
“A kwanakin baya ma Damina ya kai hari a kauyen Babbar Doka, inda ya kashe mutum biyu ciki har da wata mata da ya kona.
“Mutanen garin ne suka gudu zuwa Dansadau, wanda hakan ya kara fusata Dogo Gide.
“Sun yi arangama ne lokacin da masu karbar kudin harajin da Damina ya aiko suka hadu da yaran Dogo Gide, inda yaran Dogon suka ce a kai su wajen Damina.
“A can ne suka yi musayar wuta, inda Daminan ya tsira da raunuka zuwa wani kauye ya buya.
“Bayan kwana biyu kuma yaran Dogo Giden suka samu labarin inda yake, suka bi shi can suka kashe shi,” inji wata majiya.
Mazauna yankin sun ce yadda Damina yake yi ne ya sa Dogo Gide ya ja masa kunne ya daina kai hari yana kashe manoman da ba su ji ba, ba su gani ba, amma ya yi kunnen uwar shegu.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, wakilinmu bai samu jin ta bakin Gwamnatin Jihar Zamfara ba, saboda Kwamishinan Tsaro na Jihar, D.I.G Ibrahim Mamman Tsafe bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.
Shi ma Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Muhammad Shehu ba a same shi a waya ba. Sai dai Sanata Sa’idu Muhammad Dansadau, wanda dan asalin yankin ne ya tabbatar da lamarin.
‘Dogo Gide na neman Ali Kachalla’
Sanata Dansadau ya kara da cewa bayan kashe Damina, yanzu haka Dogo Gide yana neman Ali Kachalla ruwa a jallo.
“Yanzu haka Dogo Gide yana neman wani kasurgumin dan bindigar, Ali Kachalla.
“Wannan rikicin da ke faruwa a tsakaninsu abin murna ne a wajenmu,” inji Sanata Dansadau.
Ali Kachalla shi ne dan bindigar da ya harbo jirgin saman yakin Najeriya a watannin baya, inda direban jirgin ya tsallake rijiya da baya.