✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Riba da asarar da ke cikin katse layin waya — Masana Tsaro

Har yanzu wannan mataki bai hana ’yan ta’adda kai hare-hare ba.

Kimanin shekara shida ke nan da al’amuran tsaro suka tabarbare a jihohin Arewa maso Yamma, musamman ma jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da Sakkwato da Kebbi da kuma Jihar Neja.

Talakawa a yankuna da sassan wadannan  jihohi sun shiga tasku, inda aka addabe su da satar mutane don karbar kudin fansa da fyade ga matan aure da ’yan mata da zawarawa da kashe mutane da cinna wa gidaje da rumbuna wuta.

Kuma ’yan bindigar sun hana noma a wasu sassa, inda wasu garuruwan suka zama kufai, mazaunansu suka koma birane a matsayin ’yan gudun hijira.

A kokarin gwamnonin jihohin na ganin sun dakile wannan barazana ta ’yan bindiga da barayi, a makonnin da suka gabata, sun fito da wasu dokoki da matakai na musamman.

Wadannan matakai sun hada da katse layukan waya a Jihar Zamfara da wasu kananan hukumomin jihohin Sakkwato da Kaduna da Katsina.

Wasu matakan kuma sun hada da takaita zirga-zirgar babura da hana cin kasuwannin mako-mako da hana safarar dabbobi da itace da sauransu.

Ko yaya masana suke ganin wadannan dokoki?

Aminiya ta gana da masanin harkokin tsaro kuma mai fashin baki kan al’amuran tsaro, Dokta Yahuza Ahmad Getso, wanda ya ce dokokin da jihohin suka gindaya suna da matukar wahalar aiwatarwa.

“Sun kafa dokokin a lokuta mabambanta kuma akwai matsalolin da suka shafi tattalin arziki.

“Misali hana masu sana’ar itace da gawayi da hana babura a wasu lokuta da rufe layukan wayoyi da takaita sayar da man fetur da rufe tasoshin mota na je-ka-na-yi-ka, babu abin da hakan ya kara haifar wa jama’a sai kunci da talauci,” inji masanin.

Tsohon Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka (mai ritaya), ya tofa albarkacin bakinsa kan lamarin.

Ya ce “Duk da korafe-korafe da aka samu, wannan mataki da aka dauka na dakatar da sadarwa, ya yi tasiri matuka domin jami’an tsaro musamman sojoji sun samu damar yin aiki kwarai.

“Hakan ya yi sanadiyar kashewa da kama miyagun mutane da yawa da kuma tarwatsa sansanoninsu da dama.

Kuma an samu raguwar bata-gari (informants) wadanda suke ba miyagun bayanai game da sauran mutane da jami’an tsaro.”

Sai dai ya ce yana da kyau idan aka kara inganta abin kuma ya kasance na bai-daya.

“Kuma a fadakar da mutane cewa tilas ce ta sa haka, a ba su hakuri da kuma tallafa wa mutanen kirki masu rauni domin rage takurar,” inji Janar din.

Kan daukar matakan katse layukan waya a jihohi da aka ambata, wadansu masana kimiyya sun ce maimakon katse layukan, kamata ya yi a yi amfani da fasahar waya wajen gano maboyar ’yan ta’addan don yin maganinsu.

Masanan sun ce matakin katse wayar ba zai amfana komai ba.

Sai dai Janar Kuka-Sheka, ba haka ya kalli al’amarin ba, inda ya bayyana cewa: “A’a, masu fadar hakan suna da son rai ne kawai.

“Kamata ya yi su yi la’akari da dalilin da ya sa haka da kuma halin da aka shiga da kuma matakan da aka dauka daga farko.”

Ya ce babu makawa, wannan mataki na katse layukan waya ya yi amfani sosai.

“Kuma mun gani, kamar yadda na yi bayani a baya, sai dai kamata ya yi, a hada da wasu matakan na amfani da kimiyyar fasaha,” inji shi.

Game da katse layukan wayar, Dokta Getso ya ce akwai asara mai yawa da kamfanonin waya suke yi.

Akwai tabarbarewar tattalin arziki, domin kuwa da wayar ake gudanar da harkokin kasuwanci da na rayuwa.

“Katse waya zai ba ’yan ta’addan damar kai hare-haren sari-ka-noke a sassa da dama, har da wuraren da ba su iya zuwa a da, saboda, babu kafar sadarwar da za a sanar da jami’an tsaro, domin a kai masu dauki a kan lokaci,” inji shi.

Ya ce tun farko bai kamata a katse layukan ba, kamata ya yi a yi amfani da kimiyya domin bankado su da dakile su.

Ko me ya sa masanin tsaron ya ce haka?

Ya ce: “Mafi yawan masu aikata laifuffukan, ’yan yankin ne, ’yan asalin jihohi da kananan hukumomi da kauyukan ne, maganar sanin inda suke ba ta ma taso ba.

“Haka mafi yawan jami’an tsaro da mutanen gari da sarakuna da malaman addini, sun san inda wadannan ’yan ta’adda suke.”

Ya kara da cewa za a iya amfani da fasahar sadarwa domin dakile hare-haren.

“Amma ni kaina ina da tuhuma ga gwamnonin jihohin da ake kai hare-haren.

“Me ya sa aka dauki shekara shida ana kashe-kashe, ba a dauki irin wannan mataki ba sai yanzu?

“Mene ne dalilin da ya sa duk da cewa an san maboyarsu da inda suke, amma ba a kai masu hari na kai-tsaye sai dai harin sari-ka-noke?

“Akwai sababbin hare-hare da suka ta’azzara kuma me ake yi da matsalar rashin abinci da tsadar rayuwa a sakamakon wannan mataki?”

Kuma ya ce yaya maganar rajistar layi da aka tilasta wa ’yan kasa, cewa Hukumar Sadarwa za ta iya gano inda ake waya da wanda ya yi wayar ta wannan fasaha?

“Me ya sa idan aka saci manyan wayoyi manyan mutane ko masu mulki, ake tantance su a gano su cikin lokaci, ta amfani da kimiyyar bin diddigi (tracking)?”

Ya ce in dai wannan hukuma tana aiki a nan, to, ya kamata ta yi aiki a kan ’yan ta’adda, tunda da waya suke amfani wajen kiran ’yan uwan wadanda suka sace kuma da waya suke fadin inda ake kai masu kudin fansa.

“Don haka, rufe layukan waya ba shi ya kamata a fara yi ba. An bar jaki ne ana bugun taiki.

“Akwai kura-kurai da yawa wajen wannan mataki, domin rashin rufe wayar ya fi rufewar amfani.

“Rufe wayar ma ina ganin an yi haka ne domin a hana yada farfaganda, ko bayyana labarin a kafafen sadarwa na sada zumunta, wanda ta hanyarsu ana kai dauki ko fallasa abubuwa da dama, da ke sa jami’an tsaro daukar matakai ko don jama’a su yaba ko su fada ana yi,” inji shi.

Game da kukan cewa duk da katse layukan wayar, har yanzu ’yan ta’adda suna kai hare-hare a yankunan Sakkwato.

Janar Kuka-Sheka ya ce: “Eh, haka ne domin ba gaba daya aka dauki matakan ba, kuma haren-haren sun bambanta da wanda ake tsare mutane a kan hanya a sace  su kuma a yi ciniki domin karbar kudin fansa ta waya.”

Ko akwai wani mataki da yake ganinka ya kamata a dauka na daban, wanda zai samar da nasarar da ake bukata a yaki da ’yan ta’addan?

Janar Kuka-Sheka ya amsa  da cewa “Tunda har an baro shiri tun rani, har aka kai ga haka, babu wani mataki face hakan.

“Sai dai kuma kamata ya yi a ce an hada wannan mataki da wasu abubuwa na jinkan jama’a, domin rage radadin matakin.

“Sa’annan kuma a inganta tsaro sosai, a samar da bayanan sirri da kai hare-hare wajen ’yan ta’addan bai-daya.

“Haka kuma a yi amfani da kimiyyar sadarwa wajen gano miyagun mutanen ta hanyar hadin kai a tsakanin sassan jami’an tsaro da kuma ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki na zamani.”

Shi kuwa Dokta Gesto cewa ya yi: “Batun cewa ana ci gaba da kai hare-hare, duk da katse layukan waya, wannan wani abu ne da yake tabbatacce, idan muka lura da abin da ya faru a kananan hukumomin Rabah da Isa da Sabon Birni da wasu yankuna na Jihar Sakkwato.

Idan muka dawo wasu yankuna na kananan hukumomin Shinkafi da Moriki da Zurmi da sauransu nan ma haka.

Ba a magana kan hare-haren da aka rika kai wa kananan hukumomin Faskari, da Dandume da Sabuwa da Bakori, da wasu yankuna na Funtuwa.

Don haka, masanan sun bukaci gwamnatocin jihohin Arewa maso Yamma su kara kaimi, su samo hanyoyin da za su ba mutane tallafi da saukaka matsin rayuwa da ake fama da shi sakamkon takaita kasuwanci da katse layukan waya da sauran matakan da suka raunana hanyoyin samun abinci.

Sun kuma bukaci jami’an tsaro su kara kokari a kan aikinsu na bankado ’yan ta’adda da dakile su.