Barcelona da Real Madrid za su gwabza a wasan da zai kai daya daga cikinsu zuwa karawar karshe a Copa del Rey na kakar nan.
A jadawalin da aka raba ranar Litinin a wasan daf da karshe, Barcelona za ta kece raini da Real Madrid, yayin da Bilbao da Osasuna za su yi karon batta a daya bangaren.
- Bankuna za su ci gaba da karbar tsofaffin kudi bayan cikar wa’adin CBN – Emefiele
- Tsawa ta lalata gidaje sama da 100 a Filato
A makonnin da suka gabata ne, Barcelona ta lashe Spanish Super Cup bayan ta doke Real Madrid da ci 3-1 a Riyadh, babban birnin Saudiyya.
Karawar ta hamayya ta El Clasico za a yi ne gida da waje a Copa del Rey, inda Real za ta fara karbar bakuncin wasan farko ranar 27 ga Fabrairu, sai wasa na biyu ranar 3 ga Afirilu a Nou Camp.
A cikin watan Oktoba, Real ta doke Barca 3-1 a La Liga, sai dai kuma kungiyar Nou Camp ta bai wa ta Santiago Bernabeu tazarar maki biyar.
Kamar yadda jadawalin ya nuna, Osasuna ce za ta fara karbar bakuncin wasan farko, sannan ta ziyarci Athletic a karawa ta biyu.
Za a buga wasan karshe a Copa del Rey a filin Estadio de la Cartuja da ke birnin Sevilla a ranar 6 ga watan Mayu.