Sakamakon rashin tabuka abin-a-zo-a-gani a kakar wasa ta bana, rahotanni sun nuna akwai yiwuwar kulob din Real Madrid na Sifen ya dibar wa koci Rafa Benitez wa’adi.
Duk da yake kocin ya samu goyon bayan mahukunta kulob din tun bayan da aka yi wasan El-Classico tsakanin Madrid da FC Barcelona a ranar 21 ga watan Nuwamban bana, yanzu al’amurra sun canja bayan da yawa daga cikin ’yan kwallon ba sa ga-maciji da kocin. ’Yan kwallon sun nuna rashin gamsuwarsu da yadda kocin yake tafiyar da harkokin kulob din al’amarin da ya sanya suka fada cikin matsala.
Ya zuwa yanzu Real Madrid ce ta uku a teburin La-Liga na Sifen inda FC Barcelona da kulob din Atletico Madrid suke saman teburin da tazarar maki biyar duk da kunnen dokin da Barcelona ta yi a jere a wasanni biyun da suka gabata. Kuma yadda kulob din billareal ya doke na Madrid a ranar Lahadin da ta wuce da ci daya mai ban haushi, ya kara jefa kocin a tsaka mai wuya, inda da yawa daga cikin ’yan wasa da magoya bayan kulob din suka dawo daga rakiyarsa.
Sannan Hukumar kwallon kafa ta Sifen ta dakatar da Madrid daga ci gaba da buga gasar Kofin Sarkin Sifen da ake wa lakabi da Copa Del Rey bayan an samu kulob din da laifin sanya wani dan wasa da yake da katin gargadi har sau uku a wasan da suka yi da kulob din Cadiz, inda Madrid din ta samu nasara da ci 3-0 a wasan. Jim kadan bayan wasan ne kulob din Cadaz ya kai Madrid kara a gaban hukumar, bayan an tabbatar da laifin Madrid ne aka dage ta daga gasar.
Yanzu ya rage wa Madrid kofi daya ne da take fafatawa a kai a kakar wasa ta bana, wato kofin Zakarun Kulob-Kulob na Turai (UEFA Champions League).
A ranar Litinin da ta wuce ne aka fitar da jadawalin gasar, inda Madrid za ta hadu a kulob din Roma na Italiya a wasan zagaye na biyu da za a yi a watan Fabrairun 2016.
Yanzu dai abin da ake jira a gani shi ne, mahukunta kulob din za su kori kocin kafin a ci gaba da gasar Zakarun Kulob na Turai a watan Fabrairun badi ne ko kafin ma a shiga sabuwar shekarar 2016? Lokaci ne kadai zai tabbatar da hakan.
…Real Madrid za ta dibar wa Rafa Benitez wa’adi
Sakamakon rashin tabuka abin-a-zo-a-gani a kakar wasa ta bana, rahotanni sun nuna akwai yiwuwar kulob din Real Madrid na Sifen ya dibar wa koci Rafa…