Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sake doke Barcelona a karo ma hudu a jere, a wasan kece raini na El-Clasico.
Real Madrid ta yi bajinta, inda ta lallasa Barcelona har gida da ci 1-2 a gaban magoya bayanta a ranar Lahadi.
- Shekara 10 da kisan Ghaddafi : Gara jiya da yau a kasar Libya?
- An yi garkuwa da masu ibada suna tsaka da bauta a coci
Real Madrid ta fara jefa kwallo ne ta hannun dan wasan bayanta, David Alaba a minti na 32, sannan Lucas Vazquez ya zura kwallo ta 2 a minti 93, kafin Aguero ya warware wa Barcelona kwallo daya daga raga.
Vinicius ya taka rawar gani a wasan, inda ya zame wa ’yan wasan Barcelona matsala, inda ya dinga kai hare-hare masu hatsarin gaske.
Barcelona dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba tun bayan barin tauraronta Lionel Messi ya tafi zuwa kungiyar PSG.
Amma kocin kungiyar Ronald Koeman, ya ce ba lallai kungiyar ta iya yin bajintar da ake tunani ba sakamakon rashin fitattun ’yan wasan da ake bukata ba.