Da kyar Real Madrid ta samu maki daya bayan haduwar da aka barje gumi tsakaninta da Sevilla a daren Lahadi.
Yayin karon-battar da ya sauya fasalin teburin gasar La Liga, an tashi 2-2 a wasan mako na 35 da Real Madrid ta yi da Sevilla a filin wasa na Alfredo Di Stefano.
Sevilla ce ta fara sakada kwallo a ragar Real ta hannun dan wasanta Fernando a minti na 22, inda dan wasan Real, Marco Asensio ya samu nasarar farke mata a minti na 67 bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a zagaye na biyu na wasan.
A minti na 78 ne kuma Sevilla ta sake kara wa Real kwallo ta biyu ta hannun Ivan Rakitic a bugun fenareti wato bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Ana daf da tashi ne Real ta sake farke kwallo ta biyu da Sevilla ta jefa mata, inda wasu ke ganin Eden Hazard ne jefa kwallon yayin da wasu ke ganin cewa dan wasan Sevilla Diego Carlos ne ya ci gida.
Da wannan sakamako Real ta koma mataki na biyu a kan teburin da maki 75 daidai da na abokiyar hamayyarta, Barcelone da ke zaman ta uku a teburin.
Har yanzu dai Atletico Madrid ce ke jan ragama a saman teburun La Ligar bana da maki 77, inda a ranar Asabar suka tashi kunnen doki mara ci yayin haduwar da ta yi da Barcelona.
Kawo yanzu dai wasanni uku-uku su rage a karkare gasar ta Sfaniya a bana.