✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Real Madrid ta nuna wa Barcelona ruwa ba sa’an kwando ba ne

Madrid ta yi zaman dabaro a saman teburin La Liga.

Real Madrid ta yi galaba a kan babbar abokiyar hamayyarta Barcelona wadda ta lallasa da ci 3-1 a filin wasa na Bernabeu a ranar Lahadin nan.

Wasan wanda shi ne na tara a Gasar La Liga, ya bai wa Real Madrid damar yin zaman dabaro a saman teburin gasar da tazarar maki uku tsakaninta da Barcelona.

Madrid wadda ke kare kambun gasar La Ligar, ta yi wa Barcelona shigar wuri yayin da ta jefa mata kwallaye biyu tun kafin a tafi hutun rabin lokaci ta hannun Karim Benzema da Federico Valverde.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne Barcelona ta huce takaici inda ta zare kwallo daya ta hannun Ferran Torres saura minti bakwai a tashi wasan.

Sai dai kungiyar wadda Carlo Ancelotti ke jagoranta, ta jaddada nasararta da tabbatar da samun maki uku a wasan yayin da ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, kuma Rodrygo na kasar Brazil ya sa kwallon a koma.

Rodrygo yana murnar kwallon da ya jefa

A halin yanzu dai babu wata kungiya da ta yi galaba a kan Madrid tun da aka soma La Ligar bana, inda tuni ta hada maki 25 yayin da Barcelona da ke biye mata ta hada maki 22.