✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta lashe gasar Laliga karo na 35

Real Madrid ta lashe gasar Laliga karo na 35 a tarihi.

Real Madrid ta zama zakarar gasar Laliga kasar Spain ta bana bayan doke kungiyar kwallon kafa ta Espanyol da ci hudu da babu.

Wannan shi ne karo na 35 da Real Madrid ke lashe gasar ta Laliga.

Real Madrid ta zura wa Espanyol kwallo hudu rigis a raga ta hannun ‘yan wasanta; Rodrygo, wanda ya zura kwallo a minti na 33 da 43.

Shi kuwa Asensio ya zura kwallonsa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a minti na 55, sai Benzema da ci tasa kwallon a minti na 81.

Tuni aka nada Madrid a matsayin wadda ta lashe gasar ta shekarar 2021/2022 duk cewar akwai ragowar wasanni hudu da suka rage a gasar.

Dan wasan gaban Real Madrid, Karim Benzema ne ke kan gaba wajen zura kwallaye a raga da kwallo 26 a gasar, sai Enes Unal na Getafe da kwallo 15 da kuma Raul De Tomas, na Espanyol da kwallo 15.