Real Madrid ta yi sukuwa a kan Liverpool, yayin da Manchester City ta yi birgimar hankaka da Dortmund a gasar cin kofin zakarun turai, wato UEFA Champions League.
Real Madrid ta lallasa Liverpool da ci 3-1, inda Manchester City ta zura kwallaye 2-1 a ragar Dortmund.
- Yau za a ci gaba da gasar cin kofin zakarun Turai
- Direban Shugaba Buhari ya riga mu gidan gaskiya
- ‘Tun ina shekara bakwai mahaifina yake kwanciya da ni’
- Matsorata ne suka kai hari Shelkwatar ‘Yan sanda a Imo — Osinbajo
Vinicius Jr. ne ya fara zura wa Real Madrid kwallo a minti na 27, sai kwallo ta biyu da dan wasa Asensio ya zura a minti na 36.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne dan wasan Liverpool, Mohamed Salah, ya ramawa kungiyarsa kwallo daya a minti na 51.
Vinicius Jr. ya sake zura kwallo ta biyu a minti na 65, kuma ta zama kwallo ta karshe da ake jefa a wasan.
Real Madrid ta yi bajinta a wasan da salo nuna fifikon karfi a tsakaninta da Liverpool.
Manchester City da Dortmund
A daya bangaren kuma, dan wasan tsakiya, Kevin De Bryune ne ya jefawa kungiyarsa ta Manchester City kwallo daya a minti na 19 yayin karawarta da Dortmund ta kasar Jamus.
Dortmund ta yi kokarin zare wannan kwallo, inda dan wasan gabanta, Marco Reus ya jefa kwallo a minti na 84, inda wasan ya zamto kunnen doki.
Sai dai wankin hula ya kai wa Dortmund dare yayin da Phil Foden, ya sake zura wa Manchester City kwallo ta biyu a minti na 90, wanda ita ce kwallon karshe da aka zura a wasan da aka tashi 2-1.
A ranar 14 ga watan Afrilu, 2021 za a sake karawa tsakanin kungiyoyin, a zagaye na biyu don fidda wadanda za su zama zakarun gwajin dafi a matakin kusa da na biyun karshe.