✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta kori kocinta bayan wata 4 da daukarsa

A ranar Litinin da ta gabata ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayar da sanarwar korar kocinsa Julen Lopetegui watanni 4 kacal…

A ranar Litinin da ta gabata ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayar da sanarwar korar kocinsa Julen Lopetegui watanni 4 kacal bayan ta dauke shi a matsayin koci.

Hakan bai rasa nasaba da yadda kulob din yake tangal-tangal da kuma yadda kulob din FC Barcelona ya lallasa na Madrid da ci 5-1 a wasan El-Clasico da suka yi a ranar Lahadin da ta wuce.

Kafin wasan, Madrid ta yi wasanni biyar a jere ba tare da ta samu nasara ba.   Sannan yanzu ta yi wasanni uku a jere a gasar La-Liga ana lallasata gida da waje.

Wadannan dalilai da ma wasu ya sa mahukunta kulob din suka yanke shawarar sallamar kocin.

Sai dai jim kadan bayan sun sallami kocin sai aka maye gurbinsa da Santiago Solari, tsohon dan lwallon kulob din a matsayin wanda zai ci gaba da tafiyar da harkokin kulob din har lokacin da za a nada sabon koci.

Rahotanni sun nuna tsohon kocin Chelsea da ke Ingila Antonio Conte na daga cikin wadanda ake rade-radin za a ba dama wajen ci gaba da horar da Madrid amma ya zuwa ranar Talatar da ta wuce mahukunta kulob din ba su cimma matsaya a kansa ba.

Kawo yanzu kulob din Madrid yana matsayi na 9 ne a teburin gasar La-Liga yayin da FC Barcelona take matsayin na daya.

Idan za a tuna, tun bayan da Madrid ta sayar da dan lwallonta Cristiano Ronaldo ga kulob din Jubentus na Italiya ta shiga matsala ganin har yanzu ba ta samu magajinsa ba.