✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta kara matse wa Barcelona lamba a teburin La Liga

Real mai kwantan wasa tana da maki 45.

Real Madrid ta rage tazarar makin da ke tsakaninta da Barcelona, bayan da ta ci Valencia 2-0 a gasar La Liga ranar Alhamis a Santiago Bernabeu.

Real ta fara cin na farko ta hannu Marco Asensia a minti na 52, bayan da ya buga kwallon da kafar hagu ta fada raga.

Dan wasan Brazil, Vinicius Junior ne ya ci na biyu, kuma na 200 kenan a kungiyar.

Sai dai Valencia ta karasa wasan da ’yan kwallo 10 daga minti na 72, bayan da aka bai wa Gabriel Paulista jan kati, sakamakon dukan Vinicius da ya yi.

Tun farko Antonio Rudiger ya zura kwallo a raga amma na’urar da ke taimaka wa alkalin wasa yanke hukunci ta soke.

VAR ta ce kafin a ci kwallon Karim Benzema ya yi wa Yunus Musah keta a cikin da’irar mai tsaron raga.

An sauya Benzema a wasan wanda a lokacin da yake fita daga fili ya rike bayan cinyar kafarsa da hannunsa.

Da wannan sakamakon Real mai kwantan wasa tana da maki 45 a mataki na biyu da tazarar maki biyar tsakaninta da Barcelona ta daya mai 50.

Real Madrid za ta ziyarci Liverpool ranar 21 ga watan Fabrairu, domin buga wasan farko a zagayen ’yan 16 a Gasar Zakarun Turai ta Champions League.