✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Real Madrid ta kammala daukar Tchouaméni daga Monaco

Dan wasan ya fifita zuwa Madrid kan kowace kungiya.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kammala cinikin dan wasan tsakiyar AS Monaco, Aurelién Tchouaméni, a kan kudi Yuro miliyan 80.

Tchouaméni ya cimma yarjejeniya da Real Madrid tun sati biyu da suka wuce don sauya sheka zuwa kungiyar.

Paris Saint-Germain ta sanya kudi masu yawa fiye da Real Madrid don dauke dan wasan daga Monaco, amma dan wasan tsakiyar ya fifita zuwa Madrid kan kowace kungiya.

Kylian Mbappe ya yi yunkurin sauya ra’ayin dan wasan Faransan don rattaba wa PSG hannu tare da faasa zuwa Madrid.

Liverpool ma na daya daga cikin kungyoyin da suka nuna sha’awar daukar Aurelién Tchouaméni, amma daga karshe ba su yi nasara ba.

Real Madrid za ta sanar da daukan dan wasan da zarar an kammala gwajin lafiyarsa.