Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na dab da lashe gasar La Liga ta Spaniya karo na 34 bayan lallasa kungiyar Getafe a ranar Alhamis.
A halin yanzu, Real Madrid wadda ta lashe gasar sau 33 ce take saman teburin gasar da tazarar maki hudu bayan da mai biye mata Barcelona ta yi barin maki hudu a wasanni biyu a jere.
- Liverpool ta kwashi kashinta a hannun Manchester City
- N-Power: An kama wani yana damfarar ‘yan gudun hijira
Kafin koma-bayan da ta samu, Barcelona ce take jan zarenta a saman teburin gasar La Liga.
Barcelona ta tashi kunnen doki 2-2 da Celta Vigo kafin kungiyar Atletico Madrid ita ma ta rike ta a wasan da suka buga a makon nan, shi ma aka tashi canjaras ci 2-2.
Hakan ya ba wa Real Madrid damar darewa saman teburin a ranar Alhamis, bayan da ta yi wa kungiyar Getafe ci daya mai ban haushi.
Mai tsaron baya kuma kyaftin na kungiyar, Sergio Ramos ne ya jefa kwallon a bugun daga kai sai mai tsaron gida.