Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana aniyarta na ficewa daga cinikin dan wasan gaban PSG Kylian Mbappe, saboda rasin samun amsa daga PSG.
Tun farko dai Madrid ta yi tayin Yuro miliyan 160 a kan dan wasan, amma PSG ta ce albarka, wanda hakan ya sa Real Madrid ta sake kara Yuro miliyan 20 kudin ya koma Yuro miliyan 180, duk da haka PSG ta ki sallama dan wasan.
Real Madrid na ganin babu bukatar sayen dan wasan kan kudade masu yawa, tunda kwantaraginsa zai kare a karshen kakar wasanni.
Tuni dai Kylian Mbappe ya sanar da PSG da sauran abokan murza ledarsa cewar ba shi da sha’awar ci gaba da zama a kungiyar, inda ya nuna muradinsa na komawa Real Madrid.
In har aka wuce yammacin ranar Talata ba tare da an an daidaita a cinikin dan wasan ba, Real Madrid na da damar tattaunawa da shi kai tsaye a watan Janairun 2022, don daukar sa a kyauta.