✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta fara zawarcin kocin Bayern Munich

Tsohon kocin kulob din Real Madrid da ke Sifen da yanzu haka yake horarwa a kulob din Bayern Munich da ke Jamus Jupp Heynckes ya…

Tsohon kocin kulob din Real Madrid da ke Sifen da yanzu haka yake horarwa a kulob din Bayern Munich da ke Jamus Jupp Heynckes ya fara yunkurin komawa kulob din Madrid a matsayin koci kafin a fara kakar wasa mai zuwa.
Shi dai koci Jupp shi ne wanda ya taimakawa kulob din Bayern lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai a makon jiya bayan da kulob din ya lallasa na Borussia Dortmund da ci 2-1 a wasan karshe.
A gobe Asabar kuma kulob din zai sake fafatawa a wasan karshe na yunkurin lashe kofin kalubale na Jamus da kulob din Stuttgart kuma idan ya samu nasara zai lashe kofi na uku kenan a kakar wasa ta bana.
A ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa ne ake sa ran kocin zai bar kulob din inda tsohon kocin FC Barcelona Pep Guardiola zai maye gurbinsa.
Sai dai kulob din Real Madrid ya fara tunanin dauke Jupp ne da zarar ya bar kulob din Bayern, bayan shi ma ya bayar da sanarwar raba-gari da nasa kocin Jose Mourinho daga gobe Asabar watau 1 ga watan Yuni.
Duk da yake akwai rahotannin da suka tabbatar kulob din tuni ya shiga tattaunawa da kocin Paris Saint Germain PSG Carlos Ancelotti don maye gurbin Mourinho, amma rahotannin da ke fitowa a shekaranjiya Laraba sun tabbatar kulob din yana neman canza akala wajen dauke kocin Bayern fiye da na PSG.
A yayin da kocin PSG yake da sauran shekara guda a kwantaraginsa , shi kuwa kocin Bayern Jupp ya kammala kwantaraginsa da kulob din Jamus don haka zai fi sauki  Madrid ta dauke shi ba tare da biyan tarar ko kwabo ba fiye da kocin PSG da ke da sauran shekara guda a kwantaraginsa.
Jupp Heynckes ya taba lashewa kulob din Madrid kofin zakarun kulob-kulob na Turai a shekarar 1998.
A halin yanzu ya kasance daya daga cikin kocin da suka lashe kofin sau biyu a kulob daban-daban a Nahiyar Turai.