Real Madrid ta doke Athletic Bilbao har gida da ci 1-2 a ranar Laraba ba tare sa manyan ’yan wasanta 11 ba, sakamakon kamuwa da COVID-19.
Real Madrid ta fara zura kwallo ne a minti na 4 ta hannun dan wasan gabanta Benzema, wanda ya sake karawa a minti na 7.
- Zaben Shugaban Kasar Libya ba zai yiwu yadda aka tsara ba —Majalisa
- Kisan manoma 45: Ran Buhari ya baci matuka —Garba Shehu
A minti na 10 ne dan wasan gaban Athletic Bilbao, Sanchet ya farke kwallo daya, wanda a haka aka tashi daga wasan.
Madrid ta ziyarci filin wasa na San Mames da ke birnin Bilbao ne ba tare da ’yan wasa irin su Rodrygo, Asensio, Alaba, Marcelo, Modric, Bale, Lunin, Isco, sakamakon gwajin cutar COVID-19 da ya nuna sun kamu da ita.
Carvajal ya samu rauni, shi kuma Casemiro bai buga wasan ba saboda samun katin gargadi da yawa, Dani Ceballos kuma na murmurewa daga raunin da ya samu.
Real Madrid ta ci gaba da jan ragamar teburin Gasar Laliga na kasar Spain, inda ta ba wa Sevilla da ke ta biyu tazarar maki takwas.