A shekaranjiya Laraba ce kulob din Real Madrid da ke Sifen ya ce ya dibar wa dan kwallon gaba na kulob din Bareth Bale wa’adin nan da karshen watan Mayun bana ko dai ya nuna kwazo ko kulob din ya sayar da shi.
Gareth Bale wanda ya shafe kimanin shekara 6 a Madrid bayan da ya canja sheka daga kulob din Tottenham a shekarar 2013, a kakar wasa ta bana ya zura kwallaye 8 ne kacal a wasanni 22 da ya yi a gasar La-Liga ta Sifen inda hakan ya sa da yawa daga cikin magoya bayan kulob din suke yi masa ihu duk lokacin da yake wasa.
Magoya bayan Madrid sun dauka Gareth Bale ne zai jagoranci kulob din bayan Cristiano Ronaldo ya bar kulob din a karshen kakar wasan da ta wuce, amma abin mamaki sai Bale ya zama tamkar dan koyo inda matasan ’yan kwallo irin su Binicious Jnr da Lukas Bazkuez da Marco Assensio suka fi shi kokari.
Shugaban kulob din Florentina Perez ya tabbatar kulob din zai sayar da Bale don amfani da kudin wajen cefano zaratan ’yan kwallo a karshen kakar wasa ta bana.
Jaridar AS da ake wallafawa a Sifen ta ce kulob din Bayern Munich da ke Jamus da na Manchester United da ke Ingila suna nuna sha’awarsu a kan Gareth Bale da mai yiwuwa ya koma daya daga cikinsu idan Madrid ta rabu da shi.